Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N6.6m saboda bata son fentin jikinta

Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N6.6m saboda bata son fentin jikinta

Wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna yadda wata mata da ba a ambaci sunanta ba ta ki karbar kyautar motar alfarmar nan da ake kira 'G Wagon' saboda kawai kalar motar ba ta kwanta mata a rai ba.

Saurayin matar ya yi niyyar bata mamaki ta hanyar saya mata mota kirar 'G Wagon' a kan miliyan N66.6 tare da yi mata kwalliya da jajayen kyalle kafin a kaiwa masoyiyarsa ita a matsayin kyauta.

Domin kara armashin dabararsa ta bawa masoyiyarsa mamaki, saurayin ya yi amfani da kyalle wajen rufe idanunta tare da kama hannunta zuwa wurin da aka ajiye motar.

Bayan an bude idon budurwar domin ta yi kwalli da motar da saurayinta ya siya mata, sai kawai ta fashe da kuka.

Sabanin tunanin jama'a a kan cewa tana kukan jin dadi ne, sai ta fada cikin kuka cewa ba za ta karbi kyautar motar ba saboda ba irin kalarta take so ba.

Saurayinta, wanda ke tsaye domin ganewa idonsa irin murnan da za ta yi na samun kyautar bazata ta motar alfarma, ya matukar girgiza da jin cewa ba zata karbi kyautar motar ba saboda kawai bata son fentinta.

Cikin murna da zumudi saurayin ya shiga cikin gidansu tare da katsewa budurwar uzurinta domin ta fito ta ga motar da ya sayo mata ba tare da saninta.

Bidiyo: Budurwa ta ki karbar kyautar motar N6.6m saboda bata son fentin jikinta
G Wagon
Asali: UGC

Shi kansa saurayin ya kasa boye mamakinsa bayan masoyiyarsa ta sanar da shi cewa motar ta yi amma ba za ta iya karba ba saboda ba ta son irin kalar wacce ya sayo.

Cikin kuka ta koma cikin gidansu ta na maimaita cewa; ''ba wannan kalar nake so ba, ba irinta na ke so ba,".

Kalli faifan bidiyon a kasa;

Ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun bayyana mabanbantan ra'ayi a kan halayyar da budurwar ta nuna.

DUBA WANNAN: El-Rufa'i ya fasa kwai, ya fadi dalilin dawowar rikicin kudancin Kaduna a lokacin mulkinsa

A yayin da wasu ke ganin ta nuna rashin godiyar Allah da wadatar zuci saboda kin karbar kyautar irin wannan motar alfarma saboda kawai launinta, wasu kuwa sun bayyana cewa babu wani aibu dangane da yin hakan.

Masu ganin cewa budurwar ta yi daidai, sun kafa hujja da cewa ba don mota ta ke son saurayin ba, kuma ta nuna cewa koda mota ko babu zasu cigaba da zama tare.

Wasu daga cikin ma su irin wannan ra'ayi na ganin cewa tunda dai saurayin ya yi niyyar saya mata motar kuma har ya iya biya kudinta lakadan, sauyata zuwa launin da budurwar ke so ba wata matsala ba ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: