Da duminsa: Bayan sa'o'i 5, Hukumar DSS ta saki Ghali Na'abba
Hukumar tsaron farin kaya, watau DSS, ta saki tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na'abba bayan kwashe sa'o'i biyar a hedkwatarta yau Litinin.
Hukumar ta sammaci Na'abba ne sukan Buhari a hirar da yayi a tashar Channel TV inda bayyana yadda kungiyarsa zata samar da sabuwar Najeriya.
Kakakin kungiyar National Consultative Front NSF, Dr Tanko Yunusa, ya tabbatar da hakan ga Sahara Reporters.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Shugabannin kudancin Kaduna sun nemi na basu kudi kafin a samu zaman lafiya - El-Rufa'i
A ranar Asabar, Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gayyaci tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na'abba, kan hirar da yayi a tashar Channels ranar Alhamis kan shirye-shiryen wata sabuwar kungiya NCF domin samar da sabuwar Najeriya da kowa zai ji dadi.
Kakakin kungiyar, Dr Tanko Yunusa, ya bayyana hakan a jawabi ranar Asabar.
Ya ce tsohon Kakakin ya yanke shawarar amsa gayyatar ranar Litnin, 17 ga Agusta.
Za ku tuna cewa Ghali Na'abba ya tuhumci shugaba Muhammadu Buhari da mayar da Najeriya abinda ta zama, inda ya siffantashi a matsayin shugaba mafi gazawa a tarihin Najeriya.
Jawabin yace: "Ku sani cewa DSS a ranar Juma'a ta bayyaci shugaban NCF kuma tsohon kakaki a Najeriya, Ghali Umar Na'abba, sakamakon hirar da yayi a tashar Channels Television ranar Alhamis da manufar kungiyar NCFront na samar da Najeriya da kowa zai ji dadi.
"Amma shugabanmu, Ghali Umar Na'abba, ya yanke shawaran amsa gayyatan DSS kuma zai je hedkwatan hukumar dake Abuja ranar Litinin misalin karfe 12 na rana."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng