Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani

Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani

Hukumar kula da lamurran addinai da 'yancinsu na Amurka, ta caccaki hukuncin shekaru 10 da aka yankewa yaro mai shekaru 13 a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke Kano.

Yaron mai suna Umar Faruk, an kama shi da laifin yin kalaman batanci ga Allah a yayin da suke muhawara da wani abokinsa.

An kama shi da laifin kuma an yanke masa hukunci ne a ranar 10 ga watan Augusta, rana daya da aka yankewa mawakin Kano da ya yi wa Annabi Muhammadu kalaman izgili.

Hakazalika, alkali daya, Aliyu Kanu ne ya yankewa Yahaya da Faruk hukuncin a kotun shari'ar Musulunci.

Hukumar ta kushe dukkan hukuncin don ta ce hakan ya take hakkinsu na dan Adam.

Hukumar kula da lamurran addinai da 'yancinsu na duniya (USCIRF) ta kushe dokokin batancin na Najeriya.

USCIRF kungiya ce mai zaman kanta kuma ba ta siyasa bace wacce aka kafa a Amurka don dubawa tare da rahoto a kan duk wata barazana ga 'yancin addini.

Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani
Batanci ga Allah: Kotu ta yanke wa yaro mai shekaru 13 hukunci mai tsanani. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Kotu ta soke zaben gwamnoni na jihar Bayelsa

A wata takarda da hukumar ta yi martani a kan hukuncin, ta kushe hukuncin kisan da aka yanke wa Sharif-Aminu a kan kama shi da aka yi da laifin batanci ga Annabi Muhammad.

Kwamishinan USCIRF, Frederick Davie, ya ce, "Abun takaici ne yadda Sharif-Aminu ke fuskantar hukuncin kisa a kan bayyana abinda ya yarda da shi ta hanyar waka.

"Majalisar dattawan Amurka ya kamata ta yi gaggawar duba lamarin tare da kira ga gyara dokokin batanci."

Hannibal Uwaifo, shugaban kungiyar lauyoyin Afrika, ya kushe hukuncin kuma ya ce hakan bai yi biyayya da kundin tsarin mulki ba.

Uwaifo ya ce, "Ina kira ga antoni janar na tarayya da ya shiga lamarin kuma ya hana irin wannan kotun hukunci a Najeriya.

"Wannan kasa ce da ake satar biliyoyin naira kuma ake basu wani bangarensa don goyon baya. Daga nan sai a ce mutum ya yi batanci amma ga addinin.

"A daina yankewa matasa da kananan yara irin wannan hukuncin. Ina tunanin dole a daina domin abun dariya ne."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel