Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa

Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa

Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta sanar da mutuwar wani mutum mai suna Izuchukwu Achusim, mai shekaru 42 a tafkin wanka na wani otal a garin Onitsha.

Rundunar ta gano cewa Achusim dan kasuwa ne wanda ake zargin ya je shakatawa otal din da budurwarsa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Haruna Mohammed, ya ce an gaggauta mika mutumin asibiti mafi kusa, amma daga bisani likitan da ke aiki ya tabbatar da mutuwarsa.

Mohammed ya ce, a ranar 15 ga watan Augustan 2020, wurin karfe 8:30 na dare, rahoto daga ofishin 'yan sanda na Onitsha ya tabbatar da cewa wani mutum mai shekaru 42 mai suna Izuchukwu Achusim ya mutu a wani otal.

Achusim na da shekaru 42 kuma ya rasu ne a otal mai lamba 35 da ke Fegge a Onitsha, bayan ya je shakawata da budurwarsa.

Ya ce jami'an 'yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma an mika gawar mamacin ma'adanar gawawwaki don gano abinda ya yi ajalinsa.

"A halin yanzu ana bincikar lamarin don bankado abinda ke tattare. Rundunar na kira ga jama'a da basu iya iyo ba, da su dauka matakan kariya kafin fadawa tafki don iyo. Hakan ne kadai zai sa su tsira da miyagun kaddarori," Mohammed ya bada shawara.

Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa
Ruwa ya halaka wani mutum a otal bayan da ya je shakatawa da budurwarsa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotunan kasaitacciyar liyafar da masarautar Ibira ta shiryawa Adama Indimi da angonta

A wani labari na daban, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da mutuwar tsohon mataimakin gwamna kuma gwamnan jihar Gongola, Wilberforce Juta.

Fintiri ya ce Juta ya mutu ya rasu ne ranar Asabar, 15 ga agusta bayan gajeuwar rashin lafiya. Ya siffanta tsohon gwamnan a matsayin dattijon arziki kuma mai mutunci.

Yace: "Na samu labari cikin kaduwa da bakin cikin kan mutuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Ambasada Wilerforce Bafte Juta yau.

"Lallai, dattijon ya kasance mai sadaukar da kai da tausayi. Allah ya hutar da shi da kuma baiwa iyalinsa ikon hakurin rashin."

Legit.ng ta tuwa cewa Wilberforce Juta, wanda ya kasance mataimakin gwamnan Gongola a 1979, sannan ya zama gwamna a 1983, bayan maigidansa, Abubakar Barde, yayi murabus daga ofis.

Juta ya kasance kan mulki zuwa Oktoban 1983 da aka zabi Alhaji Bamanga Tukur matsayin gwamna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel