Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Tsohon kakakin ya yi martani

Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Tsohon kakakin ya yi martani

Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'Abba, ya tabbatar da cewa zai amsa gayyatar hukumar tsaro ta farin kaya a babban ofishinsu da me Abuja a ranar Litinin, karfe 12 na rana a kan tattaunawar da yayi da wani gidan talabijin a makon da ya gabata.

Na'abba ya yi tattaunawar ne a matsayinsa na daya daga cikin shugaban wata kungiya mai suna NCF.

A takardar da shugaban fannin yada labarai na kungiyar, Dr. Tanko Yunusa ya fitar, ya ce Na'Abba zai amsa gayyatar, duk da kuwa ya ce a hankali kasar ke barin salon mulkin farar hula.

A yayin tattaunawar, Na'Abba ya yi magana ne a kan "yadda za a kawo sabuwar Najeriya da za ta yi amfani ga kowa".

Tsohon kakakin majalisar ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin iya mulki.

Ya ce gwamnatin ta kasa shawo kan matsalar rashin aikin yi na matasa da rashin tsaron da ke kawo mace-macen 'yan Najeriya a kowacce rana.

Ya ce tabarbarewar kasar nan ya ci gaba da ta'azzara ne karkashin mulkin tare da kara yawan matalauta a Najeriya.

Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Tsohon kakakin ya yi martani
Gayyatar Na'Abba a kan caccakar Buhari: Tsohon kakakin ya yi martani. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan kasaitacciyar liyafar da masarautar Ibira ta shiryawa Adama Indimi da angonta

Za ku tuna cewa Ghali Na'abba ya tuhumci shugaba Muhammadu Buhari da mayar da Najeriya abinda ta zama, inda ya siffantashi a matsayin shugaba mafi gazawa a tarihin Najeriya.

Jawabin yace: "Ku sani cewa DSS a ranar Juma'a ta bayyaci shugaban NCF kuma tsohon kakaki a Najeriya, Ghali Umar Na'abba, sakamakon hirar da yayi a tashar Channels Television ranar Alhamis da manufar kungiyar NCFront na samar da Najeriya da kowa zai ji dadi.

"Amma shugabanmu, Ghali Umar Na'abba, ya yanke shawaran amsa gayyatan DSS kuma zai je hedkwatan hukumar dake Abuja ranar Litinin misalin karfe 12 na rana."

A makon da ya gabata, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, ya amsa tambayoyin jami'an tsaron na farin kaya a kan tattaunawar da yayi da wani gidan rediyo inda yace wani gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel