Kano: 'Yan sanda sun sake ceto matashi da yayi shekaru 15 a daure

Kano: 'Yan sanda sun sake ceto matashi da yayi shekaru 15 a daure

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta sake ceto wani mutum da mahaifinsa ya daure na tsawo shekaru 15. An daure Ibrahim Lawal tun yana da shekaru 20 a duniya.

Mahaifin Ibrahim, Lawan Sheka, wanda shine limamn babban masallacin yankin ne ya dauresa.

Limamin ya tsere bayan zuwan rundunar 'yan sanda.

An ceto Ibrahim a kwatas din Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

A halin yanzu, yana asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano don samun agajin likitoci.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya ce sun yi amfani da bayanan sirri ne da suka samu a kan halin da Ibrahim yake ciki a safiyar Lahadi.

Kwanaki biyu kafin ceto Ibrahim, 'yan sanda sun tsinkayi kwatas din Farawa da ke karamar hukumar inda suka ceto wani matashi mai shekaru 32 mai suna Ahmad Aminu, wanda mahaifinsa ya daure a kan zarginsa da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Ahmad, wanda a halin yanzu yake hannun masana kiwon lafiya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, an ceto shi ne bayan wata makwabciyarsu mai suna Rahama ta sanar da 'yan sanda halin da yake ciki.

Kano: 'Yan sanda sun sake ceto matashi da yayi shekaru 15 a daure
Kano: 'Yan sanda sun sake ceto matashi da yayi shekaru 15 a daure. Hoto daga Daily Trust
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Sojin sama sun ragargaza sansanin ISWAP, sun kashe mayaka masu yawa

A wani labari makamancin hakan, wata mata ta daure yaro maraya mai shekaru 10, mai suna Jibril Aliyu, na tsawo shekaru biyu a garken tumaki ba tare da abinci isasshe ba a jihar Kebbi.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, matar uban yaron ta dinga yi mishi tamkar ba dan Adam ba bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani a sa'o'in farko na ranar Litinin, wanda ke nuna yaron a rame har baya iya tashi tsaye saboda yunwa.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an damke wacce ake zargin yayin da aka kwantar da yaron a asibitin tunawa da Yahaya da ke Birnin Kebbi.

Wani bidiyo wanda ake zargin an daukesa a ofishin 'yan sanda a jihar, ya bayyana wacce ake zargin tana bayani ga 'yan sanda inda take musanta daure yaron.

Kamar yadda wata ma'abocin amfani da Facebook, Tukur Tacha, ya wallafa, ya ce mahaifiyar yaron ta rasu a shekarun da suka gabata kuma ana zargin marikiyarsa da ciyar da shi da ragowar abinci da kuma kashin tumaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel