Hukumar DSS ta gayyaci Ghali Na'abba don ya soki gwamnatin Buhari

Hukumar DSS ta gayyaci Ghali Na'abba don ya soki gwamnatin Buhari

Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta gayyaci tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya, Ghali Umar Na'abba, kan hirar da yayi a tashar Channels ranar Alhamis kan shirye-shiryen wata sabuwar kungiya NCF domin samar da sabuwar Najeriya da kowa zai ji dadi.

Kakakin kungiyar, Dr Tanko Yunusa, ya bayyana hakan a jawabi ranar Asabar.

Ya ce tsohon Kakakin ya yanke shawarar amsa gayyatar ranar Litnin, 17 ga Agusta.

Za ku tuna cewa Ghali Na'abba ya tuhumci shugaba Muhammadu Buhari da mayar da Najeriya abinda ta zama, inda ya siffantashi a matsayin shugaba mafi gazawa a tarihin Najeriya.

Jawabin yace: "Ku sani cewa DSS a ranar Juma'a ta bayyaci shugaban NCF kuma tsohon kakaki a Najeriya, Ghali Umar Na'abba, sakamakon hirar da yayi a tashar Channels Television ranar Alhamis da manufar kungiyar NCFront na samar da Najeriya da kowa zai ji dadi.

"Amma shugabanmu, Ghali Umar Na'abba, ya yanke shawaran amsa gayyatan DSS kuma zai je hedkwatan hukumar dake Abuja ranar Litinin misalin karfe 12 na rana."

Hukumar DSS ta gayyaci Ghali Na'abba don ya soki gwamnatin Buhari
Hukumar DSS ta gayyaci Ghali Na'abba don ya soki gwamnatin Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya

A makon da ya gabata, Hukumar lura da kafafen yada labarai a Najeriya NBC, a ranar Alhamis ta ce za ta fara hukunta duk tashar watsa labaran da ta sabawa dokokinta.

Ta gargadi kafafen watsa labarai cewa su fahimci dokoki da ka'idojin sana'ar.

Diraktan hukumar NBC na jihar Legas, Chibuike Ogwumike ya bayyana hakan a takardar da aikewa manema labarai.

Ya ce: "Sakamakon bincike ya nuna cewa kwanakin nan, wasu kafafen yada labarai sun daina aikinus na tantance kalaman mutanen da suka gayyata shirye-shiryensu inda ake zagin shugabanni da masu mulki a fili."

"Cin mutuncin shugabanninmu da manyamu da kalaman zagi ya sabawa al'adarmu. Muna ganin girman shugabanninmu kuma hakan ne al'adarmu."

"Zagi da cin mutuncin shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisar da sauran shugabanni ya sabawa al'adarmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel