Yanzu-yanzu: Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya

- Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Wilberforce Juta, ya mutu

- Juta ya mutu ya rasu ne ranar Asabar, 15 ga agusta bayan gajeuwar rashin lafiya

- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Finitiri, ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Wilberforce Juta

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanar da mutuwar tsohon mataimakin gwamna kuma gwamnan jihar Gongola, Wilberforce Juta.

Fintiri ya ce Juta ya mutu ya rasu ne ranar Asabar, 15 ga agusta bayan gajeuwar rashin lafiya.

Ya siffanta tsohon gwamnan a matsayin dattijon arziki kuma mai mutunci.

Yace: "Na samu labari cikin kaduwa da bakin cikin kan mutuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Ambasada Wilerforce Bafte Juta yau.

"Lallai, dattijon ya kasance mai sadaukar da kai da tausayi. Allah ya hutar da shi da kuma baiwa iyalinsa ikon hakurin rashin."

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya
Yanzu-yanzu: Tsohon gwamna a Najeriya ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya
Asali: UGC

KU KARANTA: Da dumi: Sabbin mutane 325 sun kamu da Coronavirus a Najeriya

Legit.ng ta tuwa cewa Wilberforce Juta, wanda ya kasance mataimakin gwamnan Gongola a 1979, sannan ya zama gwamna a 1983, bayan maigidansa, Abubakar Barde, yayi murabus daga ofis.

Juta ya kasance kan mulki zuwa Oktoban 1983 da aka zabi Alhaji Bamanga Tukur matsayin gwamna.

Ya kasance jakadan Najeriya zuwa Zimbabwe tsakanin 2000 zuwa 2004 kuma jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) har mutuwarsa.

A bangare guda, gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce manyan hafsoshin tsaro ya kamata a tuhuma kan hare-haren yan bindiga ba shugaba Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel