Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya faɗa wa shugaban hukumar sauraron ƙorafin jama'a da yaƙi da rashawa ta jihar, Muhyi Rimingado ya yi aikinsa ba tare da sani ko sabo ba.

Ganduje ya kuma fada wa Ramingado kada ya ɗaga wa kowa ƙafa wurin yaƙi da rashawa ko da ƴan fadar gwamna ne.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara hedkwatar hukumar a ranar Asabar domin duba aikin gyara da kwaskwarima da ake yi.

Kada ka raga wa kowa: Huɗubar Ganduje ga shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano
Abdullahi Ganduje. Hoto daga Daily Nigerian.
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara

A cewar Ganduje, ba zai yi wu gwamnatin tarayya ita kaɗai ta yi yaƙi da rashawa ba idan jihohi ba za su yi yaƙi da rashawar ba suma.

"Duk wanda ya faɗa tarkon hukumar zai fuskanci hukunci. Ba ruwa na. Ba zan saka baki ba koda wanene. Saboda haka kada ka ɗaga wa kowa ƙafa ko da ƴan fada na ne," a cewar Ganduje.

Ya ƙara da cewa, "Yadda masu rashawa ke ƙoƙarin daƙile ƙoƙarin hukumomin rashawa, kuma kasancewar yaƙi da rashawa ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Buhari ta saka a gaba, gwamantin tarayya ita kaɗai ba za ta iya ba, dole sai jihohi sun shiga za a samu nasara."

Da ya ke jawabin buɗe taron tunda farko, Ramingado ya yaba wa ƙoƙarin Ganduje wurin yaƙi da rashawa a jihar inda ya ce," jajircewar ka da goyon baya ne yasa hukumar mu ke cikin wadanda suka fi inganci a jihar."

"Mun zama abin koyi ga wasu jihohi a kasar nan," in ji shi.

Idan za a iya tunawa, a cikin ƴan kwanakin nan hukumar ta kwato wasu kudade da aka ware domin masu addu'o'i da wani hadimin gwamnan ya handame.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel