Kotun zaɓe ta yi watsi da ƙarar ɗan takarar AD, ta tabbatar da nasarar Diri

Kotun zaɓe ta yi watsi da ƙarar ɗan takarar AD, ta tabbatar da nasarar Diri

Kotun sauraron karar zaɓen gwamnan Bayelsa da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar Alliance for Democracy da ɗan takarar ta suka shigar na ƙallubalantar nasarar Gwamna Duoye Diri a zaɓen ranar 19 ga watan Nuwamban 2019.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne a ranar Asabar 15 ga watan Agusta kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Alƙalai uku da ke shari'ar sun amince da cewa ƙarar da Jam'iyyar ta AD da ɗan takarar Onwei Woniwei suka shigar ba ta inganci .

Kotun zaɓe ta yi watsi da ƙarar ɗan takarar AD, ta tabbatar da nasarar Diri
Kotun zaɓe ta yi watsi da ƙarar ɗan takarar AD, ta tabbatar da nasarar Diri
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Alkalin da ya yi shari'ar zaben Atiku da Buhari ya samu karin girma

Mai shari'a S.M. Owoduni da ga karanto hukuncin a madadin alƙalan uku ya ce waɗanda suka yi karar sun gaza gabatar da gamsasun hujja cewa mataimakin Diri, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya yi ƙarya a shekarunsa kuma ya gabatar da takardar kammala NYSC ta bogi.

Diri ne ya zo na biyu a zaben gwamnan da aka yi a jihar a bara amma aka rantsar da shi a matsayin gwamna bayan kotun koli to soke nasarar ɗan takarar jam'iyyar APC David Lyon da ya lashe zaben da farko.

Har yanzu dai akwai wasu kararrakin da aka shigar na ƙallubalantar nasarar Diri da kotun za ta zartar da hukunci a kai a yau Asabar.

Ku saurari cikakken rahoton ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel