Da duminsa: Sabbin yan Najeriya 329 sun kamu da Coronavirus
Hukumar Takaita Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 329 a fadin Najeriya yau Juma'a.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:49 na daren ranar Juma'a 14 ga Agustan shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta a shafinta na Twitter, ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar a jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-113
Kaduna-49
FCT-33
Plateau-24
Kano-16
DUBA WANNAN: Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Walter Carrington
Edo-15
Ogun-14
Delta-13
Osun-10
Oyo-8
Ekiti-6
Bayelsa-6
Akwa Ibom-5
Borno-4
Enugu-4
Ebonyi-3
Rivers-2
Bauchi-1
Nasarawa-1
Gombe-1
Niger-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 14 ga Agustan shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a Najeriya ya kai 48,445 .
An sallami mutum 35,998 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta kashe jimillar mutane 973.
Asali: Legit.ng