Badakalar $500m: Dan tsohon shugaban kasa zai shafe shekaru biyar a kurkuku

Badakalar $500m: Dan tsohon shugaban kasa zai shafe shekaru biyar a kurkuku

A ranar Juma'a ne kotun koli ta kasar Uganda ta zartar da hukuncin daurin shekaru biyar a kan Jose Filomeno dos Santos, dan tsohon shugaban kasa, bayan samunsa da laifin almundahana a lokacin da ya ke shugabantar asusun kudin rarar man fetur.

An fara gurfanar da Dos Santos, mai shekaru 42, a gaban kotu a watan Disamba bisa tuhumarsa da barnatar da dalar Amurka biliyan $1.5 a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018.

Ana zargin Dos Santos, wanda ake wa lakabi da 'Zenu', da laifin karkatar da dalar Amurka miliyan $500 zuwa asusun wani banki a kasar Swiss.

"Bayan samunsa da laifin aikata almundahana da kuma laifin amfani da iko ta haramtacciyar hanya, wannan kotu ta yanke ma sa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar," a cewar alkalin kotun, Joao da Cruz Pitra.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Dos Santos, wanda su ka hada da tsohon gwamnan babban bankin kasar Angola, Valter Filipe da Silva, an yanke mu su hukuncin daurin shekaru hudu zuwa shida a gidan yari.

Kotun ta zartar da hukunci a kansu bayan samunsu da laifin almundahana, barna, safarar kudi, da amfani da iko ta haramtacciyar hanya.

Badakalar $500m: Dan tsohon shugaban kasa zai shafe shekaru biyar a kurkuku
Jose Filomeno dos Santos
Asali: Twitter

Zenu ya kasance mutum na farko daga dangin tsohon shugaban kasa da aka yankewa hukuncin zaman gidan yari.

Wannan hukunci tamkar cika alkawarin da shugaban kasar Angola, Joao Lourenco, ya dauka ne na gurfanar da iyalin tsohon shugaban kasa a lokacin da ya ke yakin neman zabe a shekarar 2017.

DUBA WANNAN: Yadda batagari su ka yi wa wasu kananan 'yammata biyu fyade a gaban mahaifinsu - Rundunar 'yan sanda

A cikin watan Fabarairu ne ma su bincike a kasar Angola su ka rufe asusun banki na Isabel dos Santos, 'yar uwar Zenu, bayan an gano biliyoyi a ciki.

Ita ma an gurfanar da ita a gaban kotu bisa tuhumarta da laifukan da suka hada da safara da barnar kudaden kamfanin dillanci man fetur na kasar Angola (Sonangol) wanda ta shugabanta zamanin mulkin mahaifinta.

A lokacin gwamnatinsa, tsohon shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos, ya damka rikon ma'aikatu da hukumomi ma su maiko a hannun dangi da abokai.

Hakan ya jefa kasar Angola, mai arzikin man fetur, a cikin talauci tare da rura wutar matsalar bangaranci da kabilanci.

Yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Lourenco ke yi a yanzu haka a kasr Angola ya fi karkata ne a kan 'yan uwa da dangin tsohon shugaba Eduardo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel