Da dumi-dumi: Kungiyar Barcelona ta lallasu 8-2, lallasuwa mafi muni cikin sama da shekaru 70
Kungiyar kwallon Bayern Munich ta ci mutuncin kungiyar Barcelona da ci 8 ga 2 a wasan zarcewa kusa na da na karshe ana gasar Zakarun Turai da aka buga yau Juma'a a a birnin Lison, kasar Portugal.
Thomas Muller da Phillipe Coutinho sun samu zura kwalle biyu-biyu inda suka karya lagwon Barcelona da yiwuwar cigaba da zaman Messi a kungiyar.
Yanzu Bayern Munich za ta kara da duk wanda yayi nasara tsakanin Manchester City da Lyon gobe.
Wadanda suka zuka kwallo wa Bayern Munich sune: Thomas Muller (2), Joshua Kimmich (1), Robert Lewandowski (1), Philippe Coutinho (2), S Ganbry (1) da Ivan Preisic (1).
Na kungiyar Barca kuwa akwai Luis Suarez (1), sai David Alaba na Bayern Munich wanda ya ci gidansa.

Asali: Getty Images
Mun kawo muku rahoton cewa Mai tsaron bayan kungiyar kwallon Barcelona, Samuel Umtiti, ya kamu da cutar Coronavirus.
Kungiyar kwallon ta bayyana cewa Dan kwallon wanda ya lashe kofin duniya a 2018, ya kamu da cutar ne a jawabin da ta saki ranar Juma'a.
Umititi, wanda yake jinya kuma ba zai yi wasa da yammacin nan ba a gasar zakarun Turai inda kungiyarsa Barcelona za ta goge raini da kungiyar kwallon Bayern Munich a birnin Lisbon, Portugal.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng