Hukumar Soji ta kammala bincike kan harin da aka kaiwa Zulum, ta gargadeshi kan kalamansa

Hukumar Soji ta kammala bincike kan harin da aka kaiwa Zulum, ta gargadeshi kan kalamansa

Hukumar Sojin Najeriya ta gargadi gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kan yin kalamai marasa tushe da inganci kan jami'anta dake filin daga.

Wannan na cikin shawarwarin da kwamitin binciken da baiwa hakkin binciko gaskiyar maganar cewa Sojoji sun ajiye makamai suna noma da kiwon kifi a Baga.

Jagoran kwamitin Manjo Janar Felix Omogui, wanda shine mataimakin tiyata kwamandan rundunar Operation Lafiya Doke, ya yi hira da yan jarida ranar Juma'a a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Ya bayyana cewa wasu jami'an tsaro da ba Soja bane suka fara yayata jita-jitan kuma suka fadawa gwamnan.

Janar Felix ya bayyana cewa lokacin da suka je garin Baga gane ma idanuwansu, babu alamun wani alaman noma ko kiwon kifi da ake zargin Sojin na yi.

"Haramcin yin noma da kiwon kifi a filin daga na cikin ka'idojin aikin Soja." Yace

Hukumar Soji ta kammala bincike kan harin da aka kaiwa Zulum, ta gargadeshi kan kalamansa
Hukumar Soji ta kammala bincike kan harin da aka kaiwa Zulum
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kasar Ireland ta amince da dawowa Najeriya kudin badakalar Abacha €5.5m (N2bn)

Ya kara da cewa kwamitin binciken ta samu garin Baga cike da bama-baman da aka birne cikin kasa yadda ba za'a iya noma ba.

"Wasu jami'an tsaro yan iya yi masu neman suna maimakon hada kai da yan uwansu suke yada karerayi."

"Gwamnan Borno kuma ya amince da wadannan zarge-zargen da aka yiwa Sojojin 19 Birgade a Baga bisa kalaman da yayi kwanan nan,"

"Kalaman manyan mutane irin wannan zai iya ragewa Sojojin karfin gwiwa kuma zai iya mumunan tasiri kan yakin da ake yi da kuma cire yardar da mutane suke yiwa Sojoji." Janar Felix ya kara

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel