Yanzu yanzu: Ana gab da wasa, babban mai tsaron bayan Barcelona, Umtiti ya kamu da Coronavirus

Yanzu yanzu: Ana gab da wasa, babban mai tsaron bayan Barcelona, Umtiti ya kamu da Coronavirus

Mai tsaron bayan kungiyar kwallon Barcelona, Samuel Umtiti, ya kamu da cutar Coronavirus.

Kungiyar kwallon ta bayyana cewa Dan kwallon wanda ya lashe kofin duniya a 2018, ya kamu da cutar ne a jawabin da ta saki ranar Juma'a.

Umititi, wanda yake jinya kuma ba zai yi wasa da yammacin nan ba a gasar zakarun Turai inda kungiyarsa Barcelona za ta goge raini da kungiyar kwallon Bayern Munich a birnin Lisbon, Portugal.

Jawabin kungiyar yace: "Bayan gwajin da aka yi ranar Alhamis, babban dan wasa Samuel Umtiti ya kamu da cutar Coronavirus. Babu alamun cutar a jikinsa kuma yana cikin koshin lafiya yana killace a gida."

"Kungiyar ta sanar da hukumomi kwallo kuma an kaddamar da bibiyan wadanda sukayi mu'amala da shi saboda a gwada su."

KU KARANTA: Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya

Yanzu yanzu: Ana gab da wasa, babban mai tsaron bayan Barcelona, Umtiti ya kamu da Coronavirus
Yanzu yanzu: Ana gab da wasa, babban mai tsaron bayan Barcelona, Umtiti ya kamu da Coronavirus
Asali: Getty Images

A ranar Laraba, mun kawo muku cewa An tabbatar da wani ‘dan wasan kungiyar FC Barcelona ya kamu da cutar COVID-19 mai jawo wahalar numfashi.

Wannan labari ya zo wa kungiyar kwallon kafar da magoya bayanta ne a lokacin da ta ke shirin haduwa da Bayern Munich a Ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na yanar gizo a jiya ranar Laraba, 11 ga watan Agustan, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel