Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya

Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya

Hukumar tsaron farin kaya, DSS, a ranar Juma'a ta caccaki tsohon mataimakin gwamnan CBN, Dr Obadiah Mailafiya, inda ta siffantashi matsayin makaryaci kuma mai yada labaran bogi.

DSS, ta bayyana hakan ne a takardar da kakakinta, Peter Afunanya, ya rattafa hannu inda tace ta ji kunya mutum irin Obadiah Mailafiya wanda ke da alaka da manyan ma'aikatan gwamnati da zai iya fadawa bayanin da ya samu amma ya zabi wuce gona da iri.

Hukumar ta ce lokacin da yake ofishinsu dake Jos, ya karyata maganar da yayi amma da ya samu yanci sai ya fara cewa yana kan bakansa, Vanguard ta ruwaito.

A ranar Laraba, Hukumar DSS sammaceshi ne kan jawabin da yayi inda ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da aka saki ya fada masa cewa wani gwamnan Arewa ne shugaban yan Boko Haram.

Daga baya ta sakeshi bayan sa'o'i bakwai yana amsa tambayoyi.

DSS tace: "Abin takaici shine Mailafiya, wanda yayi ta bamu hakuri yayinda ya ziyarci ofishin hukumar dake jihar Plateau kan jawabin karyansa, amma daga baya ya sanar da duniya cewa yana kan bakansa."

"Hakazalika, hukumar tana gargadin jama'a, wadanda suke amfani da sunan siyasa wajen furta kalaman batanci su daina."

Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya
Kai makaryaci ne, kalamanka na da hadari ga Najeriya: DSS ga Obadiah Mailafiya
Asali: UGC

A bangare guda, Hukumar lura da kafafen yada labarai a Najeriya NBC, a ranar Alhamis ta ce za ta fara hukunta duk tashar watsa labaran da ta sabawa dokokinta.

Ta gargadi kafafen watsa labarai cewa su fahimci dokoki da ka'idojin sana'ar.

Diraktan hukumar NBC na jihar Legas, Chibuike Ogwumike ya bayyana hakan a takardar da aikewa manema labarai.

Hakazalika, hukumar NBC ta ci tarar wani gidan radiyo da ke jihar Legas Naira miliyan biyar.

NBC ta bayyana cewa an ci tarar gidan radiyon mai suna 'Nigeria Info 99.3FM' saboda yin amfani da wani shirinsu wajen yada labarai marasa tushe da kan iya haifar da hargitsi da tsana a tsakanin jama'a.

Gidan radiyon 'Nigeria Info' ne ya fara yada hirar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Obadiah Mailafia, ya yi zargin cewa wani gwamnan arewa ne ya ke shugabantar kungiyar Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel