Matar da ke auren maza biyu a lokaci guda kuma suke zaune gida ɗaya (Hotuna)

Matar da ke auren maza biyu a lokaci guda kuma suke zaune gida ɗaya (Hotuna)

Aure dai lamari ne mai muhimmanci a cikin al'umma na duniya daban daban inda mutane biyu da ke kaunar juna kan amince su zauna tare don soyayya da taimakon juna.

A Najeriya da mafi yawancin kasashe na Musulunci na miji ne ke auren mace kuma galibi yana iya auren mace fiye da daya idan yana da hali.

Sai dai a yanzu zamani ya canja har ta kai ga wasu matan suna auren mazaje biyu ko fiye kuma su zauna da su lafiya a gida ɗaya su haifa musu yara.

Wata mata mai amfani da dandalin sada zumunta ta wallafa hotunan ta tare da maza biyu da yara da ta ce mazanta ne kuma suna zaune lafiya.

Kenya Stevens mace mai maza biyu ta ce har yanzu tana iya tsunduma wa cikin kogin soyayya da wani idan tasu ta zo ɗaya.

Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Asali: Instagram

Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Asali: Instagram

Ta wallafa hotun mazanta biyu, Rakhem Seku, mai bawa mutane shawarwari kan zamantakewar soyayya kuma marubucin littafai.

Tana kiran su 'Hubby 1' da 'Hubby 2' wato miji na farko da miji na biyu har wasu lokutan ta ke yi musu ba'ar cewa za ta ƙara miji na uku.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar Walter Carrington

Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Asali: Instagram

Ta ce sun kwashe shekaru tare da mazan biyu kuma ta haifa musu yara har ma sun girma.

Su kan wallafa hotunansu tare a dandalin sada zumunta ta Instagram inda za a gano su cikin fara'a da annashuwa.

Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya
Asali: Instagram

Kenya ta ce mazajen nata biyu suna zaman lafiya, su kan yi yawancin harkokin su ba yau da kullum kamar gyaran mota da wasu abubuwan tare.

Ta kuma ce ba gaskiya bane ikirarin da ake yi cewa maza sun fi mata sha'awa sai dai kawai an daɗe ana dakushe mata ne shi yasa suke danne sha'awarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164