Adama Indimi da mijinta sun ziyarci surukinta a fadarsa da ke Kogi (Hotuna)
Adama Indimi da mijinta, Malik Ado-Ibrahim, sun kai wa surukinta, Ohinoyi na kasar Ebira, Alhaji (Dr) Ado Ibrahim, ziyara a fadarsa kwanaki kadan bayan daura aurensu a Maiduguri, jihar Borno.
Malik yarima ne na kasar Ebira a jihar Kogi.
An daura aurensu ne a ranar Asabar 8 ga watan Agustan shekarar 2020 misalin karfe 10 na safe.
Amma an fara bukukuwan daurin auren tun daren ranar Juma'a 7 ga watan Agusta a Maiduguri.
Malik Ado Ibrahim, shine wanda ya kafa kamfanin Bicernergy
Adama da Malik sun yi soyaya na kimanin shekara daya sannan suka yanke shawarar yin aure a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2020.
Ga wasu hotuna daga ziyarar da suka kai wa sarkin na kasar Ebira a kasa.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Asali: Twitter
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng