Hukuncin kisan saurayi mai batanci: Hisbah da limamai sun yi tsokaci

Hukuncin kisan saurayi mai batanci: Hisbah da limamai sun yi tsokaci

Majalisar limaman masallatan Juma'a na jihar Kano, sun jinjinawa hukuncin da aka yanke wa matashin da ya yi batanci ga Annabi Muhammad.

An yankewa matashi Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa ne a wata kotu da ke jihar Kano a kan wakar batanci da ya yi ga Annabi Muhammad S.A.W.

Shugaban majalisar, Muhammad Nasir Adam, kamar yadda Kano Focus ta ruwaito, ya yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar da ya sa hannu a kan takardar.

Gwamnan har yanzu bai yi martani a kan hukuncin ba.

Sharif-Aminu, mazaunin kwatas din Sharifai da ke birnin Kano, an maka shi gaban kotu ne sakamakon batanci da ya yi ga Annabi, wanda hakan ya ci karo da sashi na 382, sakin layi na 6 na dokokin shari'ar Musulunci na jihar Kano.

Mawakgin ya yi kalaman batancin ne cikin waka wacce ya watsa ta a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp a watan Maris na 2020.

Kotun shari'ar wacce ta samu shugabancin Khadi Aliyu Muhammad Kani, ta kama shi da laifin kuma ta yanke hukuncin a kashesa ta hanyar rataya.

Hukuncin kisan saurayi mai batanci: Hisbah da limamai sun yi martani
Hukuncin kisan saurayi mai batanci: Hisbah da limamai sun yi martani. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

A yayin tsokaci a kan hukuncin, Adam ya ce: "Majalisar na da tabbacin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje zai saka hannu a kan hukuncin. Ya ja kunnen Musulmi da su kiyaye yin duk wani abu da zai iya bata sunan Annabi Muhammad."

Kwamanda janar na Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Sani Ibn Sina, ya goyi bayan hukuncin.

"Hisbah hukuma ce da ke da alhakin tabbatar da an bi shari'ar Musulunci. A don haka tana goyon bayan hukuncin saboda duk wanda ya yi abinda Aminu ya yi, ya cancanci kisa. Hakan ne hukuncin Musulunci," yace.

A wani bangare, kungiyar Tijjaniyya ta barranta kanta da Yahaya Shariff Aminu, matashin jihar Kano da aka yanke wa hukuncin kisa a Kano bayan kama shi da laifin batanci da aka yi ga Annabi Muhammadu.

Wannan ne lokaci na farko da manyan kungiyoyin addini na kasar Najeriya suka yi martani a kan wannan hukuncin da aka yanke a ranar Litinin.

Shugaban majalisar zawiyoyin Tijjani da ke Kano, Mallam Muhammad Nura Arzai, ya sanar da BBC cewa, ko kadan abin da matashin ya aiwatar ba sa cikin ladubba da koyarwar Sheikh Ibrahim Inyass.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel