A fadar shugaban kasa za'ayi daurin auren diyar Buhari da hadimin Fashola

A fadar shugaban kasa za'ayi daurin auren diyar Buhari da hadimin Fashola

Daurin Auren Hanan, daya daga cikin yara matan shugaba Muhammadu Buhari zai gudana ne cikin fadar shugaban kasa, Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.

Wannan shine karo na farko da za'a gudanar da bikin daurin auren a fadar Aso Villa tun gininta a shekarar 1991.

Sahara Reporters ta ruwaito kasancewar hakan ya sanya aka yiwa auren taken "Auren Farko"

Za a yi daurin auren ne ranar 4 ga Satumba, 2020.

Hanan zata auri Muhammad Turad, babban mai baiwa tsohon gwamnan Legas kuma Ministan ayyuka na yanzu, Babatunde Raji Fashola, shawara.

Muhammad Turad 'da ne ga wani tsohon dan majalisan wakilai, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban, wanda ya wakilci mazabar Zariya tsakanin Mayun 2003 da 2007.

Hakazalika mahaifinsa ya yi takaran kujeran gwamnan Kaduna karkashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria, ACN.

Hanan ta karanci ilimin hoto a Jami’ar Ravensbourne dake Ingila.

Za ku tuna cewa A watan Juni, jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP ta caccaki Buhari kan yin amfani da fadar shugaban kasa wajen gudanar da taron majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress APC.

PDP ta siffanta hakan matsayin kololuwar rashawa, da kuma cin mutuncin gidan gwamnati da kasa.

A fadar shugaban kasa za'ayi daurin auren diyar Buhari da hadimin Fashola
A fadar shugaban kasa za'ayi daurin auren diyar Buhari da hadimin Fashola
Asali: Twitter

Tun bayan bullar cutar Korona a Febrairu, shugaba Buhari ya kasance yana gudanar da ayyukansa cikin fadar Villa, wanda ya hada da Sallar Idi karama da babbar Sallah.

A karon farko tun bayan hawansa mulki, shugaba Buhari ya yi bukin babbar Sallah a Abuja sabanin Daura, mahaifarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel