Gambari ya gana da sarakunan Anambra da gwamnansu ya dakatar saboda sun ziyarci Buhari

Gambari ya gana da sarakunan Anambra da gwamnansu ya dakatar saboda sun ziyarci Buhari

Shugaban ma'aikatar fadar shugaba Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Alhamis ya karbi baƙuncin wasu masu sarautar gargajiya daga jihar Anambra a Aso Rock Villa, Abuja.

Gwamnatin jihar Anambra a safiyar ranar Alhamis ta dakatar da sarakunan na shekara ɗaya saboda sun bar jihar ba tare da izini ba.

Masharwarcin shugaban ƙasa na musamman a kan kafafen yadda labarai, Femi Adesina ne ya sanar da ziyarar su.

Gambari ya gana da sarakunan Anambra da gwamnansu ya dakatar saboda sun ziyarci Buhari
Gambari ya gana da sarakunan Anambra da gwamnansu ya dakatar saboda sun ziyarci Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

Adesina ya ce masu sarautun gargajiyar sun bayyana godiyar su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ayyukan cigaba da ya ke yi a kasar musamman yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce Prince Arthur Eze ne ya yi wa sarakunan jagora zuwa fadar shugaban kasar.

Adesina ya ce shugaban fadar ma'aikatan fadar shugaban kasar ya ce ziyarar za ta ƙara wa shugaban ƙasar ƙaimi wurin kawo cigaba a yankin da ƙasa baki ɗaya.

"Kamar yadda aka sani a yawancin yankunan kasar nan, idan ka gode wa mutum bisa ayyukan da ya yi, hakan zai sa ya ƙara dage wa ya cigaba da aikin.

"Wannan ziyarar za ta ƙarfafawa shugaban ƙasa gwiwa ya cigaba da yi wa kasar ayyuka musamman yankin Kudu maso Gabas," kamar yadda aka ruwaito Gambari ya faɗa.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyar rasuwar tsohon jakadan kasar Amurka a Najeriya, Walter Carrington kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaban kasar cikin sanarwar da kakakinsa, Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce bayyana Carrington a matsayin "tsohon abokin Najeriya kuma kwararre da jarumin jakada."

A cikin sakon ta'aziyar da ya fitar a yammacin Laraba, Buhari ya yabi tsohon jakadan wanda ya ce, "ya goyi bayan mutanen Najeriya a filli a lokacin da suka yi fafutikan komawa demokradiyya bayan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 da marigayi Moshood Abiola ya lashe."

Buhari ya ce labarin demokradiyyar Najeriya karkashin jamhuriyya ta hudu ba za ta taba cika ba ba tare da an ambacii jarumai irinsu Ambasada Carrington.

"A madadin iyalai na, gwamnati da al'ummar Najeriya, Ina mika taaziya ta ga iyalan mamacin, abokansa, masu goyon bayansa da gwamnati da al'ummar kasar Amurka," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164