Matashi ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa mai shekara 6 a Bauchi

Matashi ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa mai shekara 6 a Bauchi

Ƴan sanda a jihar Bauchi sun kama wani matashi ɗan shekara 18 ɗalibin Kwalejin Ilimi da Shari'a ta AD Rufai, Muhammad Isa saboda garkuwa da ɗan makwabcinsa.

Yan sandan sun gabatar da wanda ake zargin ne tare da wasu da ake zargi da fashi da makami, fyaɗe, safarar miyagun kwayoyi da wallafa kuɗin jabu a hedkwatar ƴan sanda a ranar Alhamis 13 ga watan Agusta.

Rahotanni sun ce an kama Isa ne tare da abokansa saboda sace ɗan makwabcinsa a Anguwan Borno da ake kira Jaja inda suke nemi a biya kuɗin fansa Naira miliyan 2.6.

Matashi ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa mai shekara 6 a Bauchi
Matashi ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa mai shekara 6 a Bauchi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun tare hanya suna yi wa matafiya fashi a kusa a Maiduguri

Ɗalibin da ke karatun koyan Shari'a ya yi iƙirarin cewa wani abokinsa mai shekara 18, Abdulgafar Adamu ne ya koya masa wannan harkar inda ya ƙara da cewa yana neman kudin ne don ya fara aikin tela.

Isa ya ce;

"Lokacin da Abdulgafar ya faɗa min abinda za muyi, na amince nan take. Mun sace yaron kuma na kai shi gidan mu. Na yi wa iyaye na ƙarya cewa mahaifiyar yaron ta yi hatsari kuma an kwantar da ita a asibiti," kamar yadda ya faɗa cikin kuka.

"Na koya ɗinki har na buɗe shago amma abubuwa sun min wahala annobar korona kuma ina neman kudi domin in fara sana'a ta. Na tambayi mahaifi na ya taimaka min da jari amma ya ce ba shi da kudi."

Isa ya ce Abdulgafar ya kira wani Usman Muhammad mai shekaru 16 ɗan makarantar sakandare ta Fomwan a Bauchi yayin da suke tsara sace yaron.

"Na kira wani yaro Abubakar Mohammed da na sani sosai ya raka ni in siyo 'donot' sannan muka kai yaron gidan Usman muka boƴe shi a nan."

Jagoransu Abdulgafar ya ce dukkan abokansa sun amince da abinda ya shirya a lokacin da ya faɗa musu ciki har da wani Ahmed Usman mai shekaru 15.

A bangarensa, Ahmed ya ce;

"Daga baya na yi nadamar abinda na aikata amma ban samu kwarin gwiwar fada wa iyaye na ba ko wani daban."

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi, Mr Lawan Tanko Jimeta ya shaidawa manema labarai cewa za a gabatar da wadanda ake zargin a kotu idan an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel