Majalisar Koli NJC ta bukaci Buhari ya nada sabbin Alkalai 22
Majalisar koli ta shari’a NJC ta zabi wasu Alkalai 22 da take son shugaba Buhari ya nada matsayin sabbin Alkalan kotunan tarayya da jihohi.
Majalisar, a jawabin da ta saki ranar Alhamis, ta gargadi wani Alkali kan tuhumar da ake masa yayinda tayi watsi da zargin da ake yiwa wasu 16.
Jawabin yace: “Majalisar ta yanke shawaran aika wasikar gargadi ga Hon. Justice K. N. Ogbonnaya na babban kotun birnin tarayya.
Ga jerin wadanda Majalisar tayi watsi da zarge-zargen da ake musu:
Hon. Justice Ayodele Daramola, babban Alkali jihar Ekiti
Sulyman Kawu, babban Alkalin jihar Kwara
I. N. Oweibo, babban kotun jihar Legas
Hadiza R. Shagari, babbar kotun jihar Legas
Ijeoma L. Ojukwu, babbar kotun jihar Legas
Ambrose Lewis-Allagoa, babbar kotun jihar Legas
B. A. Oke-Lawal, babbar kotun jihar Legas
O. A. Ogala, babbar kotun jihar Legas
Hon. Justice Augusta Uche Kingsley-Chukwu, babbar kotun jihar Rivers
Hon. Justice Mustapha A. Ramat, babbar kotun jihar Nasarawa
Hon. Justices M. M. Ladan, babbar kotun jihar Kaduna
Muhammed Lawal Bello babbar kotun jihar Rivers
Hon. Justice Adamu M. Kafin babbar kotun jihar Bauchi
Hon. Justice L. M. Boufini, babbar kotun jihar Bayelsa
Hon. Kadi Goni Kur, kotun daukaka kara ta Shari’a, Borno
Hakazalika, kwamitin ta amince da rahoton kwamitin tantance Alkalai kuma ta zabi Alkalai 22 matsayin Alkalan kotun koli, manyan kotunan jihohi, kotu Shari’a, dss.
Hakazalika majalisar ta karbi sakon ritayan Alkalai 13 da mutuwan Alkalai 6.“

Asali: UGC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng