Dalilin da ya yasa aka daina samun masu Korona da yawa a Najeriya - NCDC
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce dalilin da yasa aka daina samun masu cutar Korona da yawa a Najeriya shine rashin gwada mutane da yawa a jihohi.
Diraktan hukumar NCDC, Dr Chikwe Ihekwewazu, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja yayin hirar kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da COVID-19 da jaridar.
Ihekwaezu wanda ya samu wakilcin, Mrs Elsie Ilori ya ce ba a amfani da cibiyoyin gwaji kamar da ya kamata kuma jihohi ba sa karban samfurin mutane domin gwaji.
"Kamar yadda aka fadi tun lokacin hutun Sallah, adadin sabbin masu kamuwa da cutar yanzu yayi kasa idan aka hada da wanda ake samu kafin Sallah, kuma haka ba wai babu masu cutar bane, kawai saboda ba ma karban isassun samfuri ne."
"Idan kuka lura, adadin samfurin da aka karba lokacin Sallah babu yawa, kuma mun san saboda lokacin hutu ne." Ya ce
Diraktan ya yi bayanin cewa hukumar na son a samu rumfar karban samfuri a kowace karamar hukuma a kasa.
"Ranar Litnin, mun yi jawabin cewa akwai kananan hukumomi 85 da babu samfurin da aka dauka, kuma bamu taba gwaji ba, amma idan muka samu rumfunan karban samfura a wadannan kananan hukumomi, za'a iya gwaji."
"Saboda haka ina kira ga jihohi su gaggauta yin gwaji kuma yan Najeriya su fito a gwada su." Ya kara

Asali: Facebook
A bangare guda, Hukumar takaita yacuwar Cututtuka a Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 453 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba 12 ga Agusta, 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta a shafinta na Twitter, ta bayyana yadda wadanda suka kamu a jihohin Najeriya kamar haka:
Lagos-113
FCT-72
Plateau-59
Enugu-55
Kaduna-38
Ondo-32
Osun-26
Ebonyi-20
Ogun-9
Delta-8
Borno-7
Akwa Ibom-6
Oyo-5
Bauchi-1
Kano-1
Ekiti-1
Jimilla kamuwa - 47, 743
Jimillan waraka - 33,943
Jimillan wafati - 956
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng