Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Ukuru, sun kashe mutum 14 sun kuma sace shanu
- Ƴan bindiga sun kai hari kauyen Ukuru a karamar hukumar Mariga na jihar Niger da ke arewa maso yammacin kasar
- 'Yan bindigan sun kashe mutane 14 sun kuma raunatta biyar tare da sace shanu masu yawa
- Jami'an ƴan sanda da 'yan kungiyar sa kai sun bi sahun maharan da nufin kamo su don su fuskanci hukunci
Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta ce an ƴan bindiga sun kashe mutane 14 a ƙauyen Ukuru da ke ƙaramar hukumar Mariga na jihar.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Minna babban birnin jihar.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi
Abiodun ya ce a ranar 12 ga watan Augusta kimanin karfe 3.30 na rana an sanar da rundunar cewa ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Ukuru inda suka bude wa mutane wuta suka sace shanu.
Ya ce a ƙarshen harin, an tabbatar da cewa mutane 14 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu mutane biyar suka samu rauni daban daban-daban.
Ya ce waɗanda aka raunata ɗin suna babban asibitin garin Mariga suna karbar magani.
Mai magana da yawun ƴan sandan ya kara da cewa jami'an rundunar da mafarauta sun bazama domin bin sahun maharan da niyyar kamo su su fuskanci doka..
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko a ranar Talata sun kafa shinge suka kuma rika yi wa matafiya fashi a hanyar Maiduguri zuwa Magumeri kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban mafarauta a jihar, Bunu Bukar, ya ce, "Maharan ba su shiga garin kuma ba su harbi kowa ba; kuma a wajen gari kawai suka tsaya suna tare motoccin da ke shiga da fita.
"A zuwa yammacin jiya Talata, wasu daga cikin maharan sun tafi amma wasu suna nan, kimanin kilomita 40 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno - suna tare motocci suna yi wa fasinjoji fashi."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng