Rabuwan kai tsakanin kabilar Igbo: Biyafara muke so, babu ruwanmu da kujeran shugaban kasa - Dattawan Biyafara

Rabuwan kai tsakanin kabilar Igbo: Biyafara muke so, babu ruwanmu da kujeran shugaban kasa - Dattawan Biyafara

Majalisar dattawan Biyafara, a jiya, ta yi watsi da jawabin kungiyar Ohanaeze Ndigbo da wasu yan siyasan kabilar Igbo cewa shugabancin kasan Najeriya suke a 2023 ba ballewa daga Najeriya ba.

Majalisar ta bayyana matsayarta ne a takardar da ta saki bayan ganawar wata-wata karkashin jagorancin shugabanta, Cif Solomon Ordu Chukwu, da aka saba yi a Owerri, babbar birnin jihar Imo.

Dattawan sun bayyana cewa abinda kabilar Igbo ke nema yanzu shine sauyin kasar gaba daya, ba sauyin wani mutum daya ko shugaba ba.

A Takardar da Diraktan yada labaran kungiyar, Chris Mocha, ya rattaba hannun, dattawan sun yi watsi da matsayar Ohanaeze Ndigbo, inda suke ce "Yan kabilar Igbo sun sha bakar wahalan hannun yan Najeriya."

Ya ce duk da cewa Dr Nnamdi Azikwe yayi yakin neman yancin Najeriya a 1960, an hanashi jagorantar kasar.

"Wadanda ke dogewa kan hadin kan Najeriya sun jahilci tarihi ne ko kuma suna amfana da wannan muguwar gwamnati ko kuma kawai basu son gaskiya kuma ba su da tunani da hangen nesa." Datttawan suka ce.

Dattawan sun yi kira ga Ohanaeze Ndigbo da yan siyasa kasar Igbo cewa su daina fadawa duniya yakin neman shugaban kasa dan Igbo abune da yankin tayi ittifaki a akai, saboda kashi 95 cikin 100 na Igbo sun fidda tsammani daga Najeriya.

KU KARANTA: Baga: Buratai ya kaddamar da bincike cikin zargin manyan Soji da yin noma da suna maimakon yaki

Rabuwan kai tsakanin kabilar Igbo: Biyafara muke so, babu ruwanmu da kujeran shugaban kasa - Dattawan Biyafara
Dattawan Biyafara
Asali: UGC

A bangare guda, Kungiyar yan kabilar Igbo a Najeriya, Ohanaeze NdIgbo ta bayyana cewa shugabanci kasa kawai take sha'awa ba ballewa daga Najeriya ba da wasu ke ta ikirari.

Kungiyar ta jaddada cewa lallai shugabancin kasa a 2023 hakki ne yan yankin kudu maso gabas, ba alfarma ba.

Shugaban kungiyar Ohaneze NdiIgbo, shiyar jihar Anambara, Cif Damian Okeke-Ogene, ya bayyana hakan yayinda yake hira da manema labarai a taron kungiyar da sukayi.

Ya ce shugabannin kungiyar basu baiwa kowani mutum ko kungiyar aikin neman ballewa daga Najeriya ba amma kawai shugaban kasa dan kabilar Igbo suke so a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel