Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa

Rikicin shugabanci da iko tsakanin Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano da masu sarautar garagjiya na jihar yana kara kamari.

Obiano ya dakatar da masu sarautar gargajiya 12 a jihar sakamakon ziyarar da suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon da ya gabata.

Ya dakatar da wani basarake mai suna Igwe Peter Uyanwa, a kan zarginsa da yake da kai korafi daga yankinsa. Ya kara da janye shaidar amincewa ta basaraken.

Dakatarwar ta shekara daya da aka yi wa masu sarautar, kamar yadda takardar ta ce, an yi ta ne saboda ziyarar da suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da izininsa ba ko amincewarsa.

An sanar da dakatarwar ne ta wata wasika da aka tura ga masarautun gargajiyar da ke fadin jihar Anambra, mai kwanan wata 11 ga Augustan 2020, ta hannun kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Greg Obi.

Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa
Ziyartar Buhari: Gwamnan PDP ya dakatar da masu sarauta 12 a jiharsa. Hoto daga The Nation
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnonin arewa sun yi martani a kan zarginsu da hannu a Boko Haram

Masu sarautar da abun ya shafa sune: Igwe Alex Edozieuno na Mkpunando; Igwe Mark Anthony Okonkwo na Alor; Igwe Chukuwma Bob Vincent Orji na Ezinifite; Igwe Engr G.B.C Mbakwe na Abacha; Igwe Chijioke Nwankwo na Nawfia and Igwe Nkeli Nelly na Igbariam.

Sauran sun hada da: Igwe Anthony Onyekwere na Owelle; Igwe A. N Onwuneme na Ikenga; Igwe Simon Ikechukwu Chidubem na Umumbo; Igwe S. O Uche na Ezira; Igwe Dr Emeka Ilouno na Ifitedunu da Igwe Peter Ikegbunem Udoji na Eziagulu Otu.

Wasikar dakatarwa an tura ta ne ga Obi na Onitsha, Alfred Achebe, wanda shine shugaban majalisar sarakunan jihar Anambra, kwamsihinan 'yan sanda da kuma daraktan hukumar jami'an tsaro ta farin kaya.

Obiano ya ja kunnensu da su daina bayyana kansu a matsayin sarakunan gargajiya kuma su gujewa bayyana a hakan a yankinsu.

Takardar ta bayyana kwace matsayinsu na 'yan majalisar sarakuna ta jihar tare da soke wasikar daukarsu aiki daga gwamnatin jihar.

Gwamnatin ta kara da cewa, za a iya dage dakatarwar zuwa karshen shekarar nan, a sabunta ta ko kuma kara ta, duk hakan ya dogara ne da yadda suka ci gaba da al'amuransu.

Amma kuma, uku daga cikin masu sarautar gargajiyar sun kwatanta hukuncin gwamnatin da abun takaici.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel