Wahalar samun wurin binne mutane ta tayar da hankalin al'umma a Kano
A wani rahoto da sashen Hausa na jaridar BBC ya ruwaito, masu kula da makabartu a jihar Kano, sun bayyana damuwa a kan yadda wuraren binne matattu suka yi karanci.
Masu aiki a makarbatu irin ta Kofar Mazugal da ke kwaryar birnin Kano, sun koka dangane da yadda suke fama da karancin wuraren binne mamata.
Yayin ganawa da manema labarai, masu kula da makarbatun sun ba da shaidar yadda a wasu lokutan suke hada gawar mutum biyu a kabari daya saboda cikar kwari da makarbatun suka yi
An ruwaito cewa, wasu daga cikin hanyoyin da ake bi a cikin makabartun na kara tsukewa a yayin da wasu kaburburan ke manne da juna saboda filin da ke tsakaninsu ba shi da yalwa.

Asali: Twitter
Shugaban masu kula da makabartar Kara da ke kofar Mazugal, Malam Danbaba Muhammad, ya kirayi gwamnatin jihar da ta kawo daukin samar da sabbin makabartu a unguwanni da ke Kano.
Malam Danbaba ya ce a yanzu a tsakanin kaburbura kadai suke iya binne gawa sanadiyar yadda makabartar ta cika makil.
“Tabbas muna fama da matsaloli a makabartun mu; a wasu lokutan sai mun sha lalube kafin gano inda za mu binne gawa.
“Wani lokaci idan mun binne gawa, sai mu riski wata gawar lafiya kalau babu abinda ya same ta, sai mu yi kasa da ita mu dora wata gawar a kanta.
“A wasu lokutan kuma kasusuwa kadai za mu tarar, sai mu baje su ma shimfida wata gawar a kai,” inji shi.
KARANTA KUMA: Jihohin Arewa 3 za su fuskanci ambaliyar ruwa - NEMA
Ya ce wannan lamari na karancin wurin binne mamata abin tayar da hankali ne musamman idan aka yi la’akari da yadda gwamnati ba ta samar da wata mafita ba.
Irin hake ce ta ke kasancewa a makabartar Gidan Gona da ke karamar hukumar Tarauni, inda wani daga cikin masu kula da ita ya bukaci a sakaya sunansa.
Ya ce su na shan bakar wahala kafin su iya samun filin da za su binne gawa sanadiyar cika da makabartar ta yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng