Jihohin Arewa 3 za su fuskanci ambaliyar ruwa - NEMA

Jihohin Arewa 3 za su fuskanci ambaliyar ruwa - NEMA

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa, akalla jihohi 3 na yankin Arewa maso Yamma za su fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da yake sauka a daminar bana.

A rahoton da Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar a ranar Laraba, ya nuna cewa jihohin za su fuskanci wannan musiba sanadiyar ruwan da ke sauka fiye da kima.

Masana dai sun bayyana cewa irin wannan ruwan sama alama ce ta tasirin sauyin yanayi a kan wasu kasashen Afrika ciki har da Najeriya.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta yi gargadi tare da ankarar da wasu jihohin uku a kan barazanar da ke tunkaro su.

Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa
Asali: UGC

NEMA ta ce al’ummar jihohin Zamfara, Sakkwato da kuma Kebbi, su kasance cikin shirin fuskantar ambaliyar a sakamakon ruwan saman da ke sauka tamkar da bakin kwarya a daminar bana.

Sanarwar hakan ta fito ne cikin bayanan da Daraktan NEMA, AVM Muhammad Alhaji Muhammad, ya yi a wani taron wayar da kan al’umma da aka gudanar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Alhaji Muhammad wanda shugaban sashen tsare-tsare, bincike da kuma hasashen yanayi na hukumar, Tukur Abubakar ya wakilta, ya ce ya zama tilas ga mazauna yankin su yi taka-tsantsan game da bala'in da ya tunkaro su.

Haka kuma hukumar NEMA cikin wani rahoto Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta kasa NIMET ta fitar, ta ce kananan hukumomi 20 daga cikin 44 na jihar Kano za su fuskanci barazanar ambaliyar a bana.

KARANTA KUMA: An daure sojan Najeriya da ya kashe ma'aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya

Jami’in NEMA na reshen jihar Kano, Sunusi Ado, shi ne ya sanar da hakan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Alhaji Sunusi ya bayyana ne a taron masu ruwa da tsaki kan wayar da kai da aka gudanar dangane da hasashen ruwan sama na bana.

Jerin kananan hukumomin da aka yi hasashen aukuwar wannan musiba a cikinsu sun hadar da Gwale, Dawakin Kudu, Warawa, Rimin Gado, Gezawa, Garun Malam, Tarauni, Nasarawa, Kumbutso da Bebeji.

Sauran kananan hukumomin sun hadar da; Gaya, Shanono, Gwarzo, Ungogo, Gabasawa, Dambatta, Kabo, Kumbotso, Kura da Karamar Hukumar Birni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel