Ka hallastawa ƴan Najeriya mallakar AK47 - Ortom ga Buhari

Ka hallastawa ƴan Najeriya mallakar AK47 - Ortom ga Buhari

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta bawa ƴan Najeriya na gari lasisin mallakar manyan bindigu kamar AK47 a matsayin matakin ƴaki da ƙallubalen tsaro a ƙasar.

Gwamnan ya ce a ɗauki tsauraran matakai da dokoki da suka dace domin hana safarar bindigun ta haramtattun hanya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Wannan da wasu bukatun duk suna dauke ne cikin batutuwan da gwamnan ya gabatar a wani ƙasida da ya gabatar a ranar Talata yayin wani taron intanet da Cibiyar Shugabanci tare da hadin gwiwar NGF suka hada.

Ka hallastawa ƴan Najeriya mallakar AK47: Ortom ga Buhari
Ka hallastawa ƴan Najeriya mallakar AK47: Ortom ga Buhari
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

A cikin ƙasidar da ya gabatar, Ortom yace ya zama dole gwamnatoci a dukkan matakai su amince cewa rashin tsaro babban barazana ce ga cigaban kasar kuma su dage don dakile ta.

Ya kuma bayar da shawarar a rika bawa hukumomin tsaro isassun kudaden horaswa da zai taimaka musu wurin yaki da rashin tsaro a zamanance.

Gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya ta rungumi tsarin gina wuraren kiwon dabobbi na zamani kuma ya shawarce ta da kafa dokar hana kiwo a fili a kasar.

A cewar sanarwa da babban sakataren yadda labaran gwamnan, Terver Akase ya fitar, Ortom ya kuma bayar da shawarar a inganta darajar ilimi da wayar da kan mutane musamman matasa don hakan zai sa suyi watsi da halaye marasa kyau.

A wani labarin, kungiyar gwamnonin arewa a ranar Laraba ta yi kira ga cibiyoyin tsaro da su binciki zargin da tsohon mataimakin shugaban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, na cewa "daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya".

A wata takarda da aka fitar a Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.

Takardar ta ce kungiyar, wacce ke aiki tare da gwamnatin tarayya, jami'an tsaro, yankuna, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da na addinai, don kawo karshen ta'addanci a yankin, tana bukatar bincikar ikirarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel