Na siyar da jinjirina ne don biyan kudin asibitin matata - Magidanci

Na siyar da jinjirina ne don biyan kudin asibitin matata - Magidanci

'Yan sandan jihar Ribas sun damke wani mutum da ake zarginsa da siyar da jinjirinsa bayan sa'o'i kadan da haihuwarsa.

Izuchukwu Okoye ya siyar da yaron ne a kan kudi N600,000 kuma ya sanar da 'yan uwansa cewa jinjirin ya rasu bayan sa'o'i kadan da haihuwarsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya sanar da manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar wata Lahadi a Igwuruta, karamar hukumar Obio Akpor ta jihar.

Ya kara da cewa ma'aikatan jinya sun karba haihuwar jinjirin a wani wurin siyar da jarirai amma an kama su tare da wanda ake zargin.

"Jami'an na musamman na yaki da fashi da makami sun yi amfani da bayanan sirri inda suka bankado wani wurin siyar da jarirai a Igwuruta inda aka samo jinjirin kwana daya wanda aka siyar bayan sa'o'i kadan da haihuwarsa," Omoni yace.

Okoye ya ce, ya yanke hukuncin siyar da jinjirin ne don ya biya kudin asibiti na matarsa. Ya kara da cewa matarsa ta zubar da jini bayan haihuwar da tayi.

A halin yanzu an mika jinjirin hannun mahaifiyarsa, 'yan sanda suka ce.

Na siyar da jinjirina ne don biyan kudin asibitin matata - Magidanci
Na siyar da jinjirina ne don biyan kudin asibitin matata - Magidanci. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da cewa tana bincike a kan wani tsoho mai shekaru 67, da kuma wasu mutum biyu a kan zargin su da ake da killace wata yarinya mai shekaru 11 suna yi mata fyade.

Ana zargin mutum ukun da yin lalata da yarinyar na dogon lokaci inda suke karba-karba da ita a babban birnin jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, ya ce tsohon ya rika amsar kudi daga hannun wani mutum da ke zuwa ya dauki karamar yarinyar a mota ya tafi da ita don lalata.

"A yanzu akwai wani wanda alama ke nuna cewa yana zuwa wurin dattijon yana daukar yarinyar a mota yana kaita wani wuri inda yake lalata da ita," DSP David Misal yace.

A halin yanzu an fara bin sahun mai motar don kama shi. Dan sandan ya ce tsohon he ya fara tsintar karamar yarinyar a tashar motar birnin Jalingo, kuma ya ajiyeta a hannunsa na tsawon watanni uku.

"Tsohon yana aikin gadi a wani gidan mai inda ya shigar da ita yake lalata da ita na kusan wata uku. Amma ba shi kadai bane."

David Misal ya ce tsohon ya kara da gayyato abokansa biyu wadanda suka rika zuwa suna yi mata fyade kafin asiri ya tonu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel