Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Zulum ya naɗa sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

Gwamnan Borno Babagana Zulum ya amince da nadin Farfesa Isa Hussaini Marte a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.

Mai magana da yawun gwaman, Malam Isa Gusau ne ya sanar da nadin a ranar Laraba da yamma kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Nadin zai maye gurbin da tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnan, Dr Babagana Wakil da ya rasu a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2020 ya bari.

Zulum ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa
Zulum ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu

Gusau ya ce ana sa ran sabon shugaban maaikatan, wanda dama kwamishina ne a fadar Zulum zai mika tsohon mukaminsa ga Dr Babagana Mustapha Mallumbe, wanda ya yanzu zai koma Maaikatar Ilimin makarantun gaba da sakandare, Kimiyya, Fasaha da Kirkire kirkire.

"Zulum ya zabi Marte ne saboda kwarewarsa, jajircewa da kaunar samar da cigaba wanda suka dace da tsarin gwamnan da kuma gaskiya da rikon amana," a cewar Gusau.

Marte Farfesa ne a bangaren Pharmacology da ya kware a kan binciken ciwon daji.

Zulum zai rantsar da sabon shugaban fadar ma'aikatan a ranar Litinin 17 ga watan Agustan shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel