Kada ku biyo dabi'armu, mun yi son kai, mun ji kunya - Ortom ga matasan Najeriya

Kada ku biyo dabi'armu, mun yi son kai, mun ji kunya - Ortom ga matasan Najeriya

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba ya ce shugabannin kasar nan sun ji kunya kuma sun kunyata Najeriya. Ya zama wajibi su fara neman gafara daga Allah.

Ya bayyana hakan ne a taron murnar zagayowar ranar Matasa ta duniya da aka yi a Makurdi, babbar birnin jihar.

Gwamnan ya bayyana yaki da rashawa da gwamnatin tarayya ke yi a matsayin zabe da son ganin bayan wasu.

"Bari in fadi a nan cewa shugabannin kasar nan sun ji kunya, har da ni." Ortom ya bayyanawa matasa

"Babban abin kunya ne ga mu shugabanni, wajibi ne mu nemi gafara daga Allah. Kuma ina baku shawara kada ku biyo dabi'armu. San kai babban kalubale ne."

"Abubuwan da mukeyi basu dace ba, Akwai babban kalubale. Akwai wadanda doka bata aiki a kansu. akwai shanayen da baka isa ka taba ba, ko da sunyi abubuwa mara kyau, ba a isa a taba su ba."

"Mutane na sace biliyoyi kuma ana kallonsu babu yadda aka iya da su amma ana daure wadanda sukayi satan kaza."

Mun kunyata kasarmu, mun ji kunya, gafarar Allah kawai ya kamata mu nema - Gwamnan Benue ga yan siyasan Najeriya
Gwamnan Benue ga yan siyasan Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar tsaron farin kaya watau DSS, ta saki Dr Obadiah Mailafiya bayan sa'o'i bakwai ana yi masa tambayoyi

Duk da haka Gwamnan ya ce idan Ubangiji ya bashi dama, yana son kwashe shekaru 90 kacal ne a duniya.

Gwamnan zai cika shekaru 60 a duniya a 2021, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng