Atiku ya kaddamar da gidan TV na yanar gizo don tallata manufofinsa
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kaddamar da gidan talabijin na yanar gizo da zai rika amfani da shi wurin yadda ayyukansa na siyasa da harkokin yau da kullum.
An haska bidiyon tsohon mataimakin shugaban kasar yana jawabi game da manufofinsa da tsare tsare a wurin taron da aka yi a Five Star Bristol Hotel da ke Kano.
Dan Atiku da wasu yan siyasa na kusa da shi musamman 'yan jam'iyyar PDP ne suka wakilce shi a wurin taron.
Hajiya Baraka Sani, tsohuwar kwamishinan ayyukan noma na jihar Kano kuma maishawarciyar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na musamman ce ta kaddamar da gidan talabijin din.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Miji ya kashe kansa saboda matarsa ta ƙi bari ya kusance ta watanni 22 bayan aurensu
Baraka Sani ta ce ‘Atiku TV’ sabon salo ne da zai sauya yadda Atiku ke isar da sakonsa ga mutane daga tsohon yayi na analogue zuwa sabon samfurin zamani na digital.
Ta yi bayanin cewa za a rika wallafa sakonnin Atiku a rumbun bidiyon intanet ta YouTube daga nan kuma a yadda zuwa dandalin sada zumunta kamar WhatsApp, Facebook, Twitter, Instagram da sauransu.
Sanata mai wakiltan Kano ta Arewa, Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya ce yan siyasa da dama za su fara kwaikwayon tsarin Atiku.
"A kasashen da suka cigaba, mutane na zaune daga gidajensu suke kallon kamfe din yan siyasa a talabijin, ba dole sai ka dauki motocci masu yawa ka fara zirga zirga daga wannan kauye zuwa wannan ba.
"Kamfe ta kafofin sadarwar zamani zai sa mutane su gane ainihin tsare tsaren ka yadda za su iya tirke ka idan ka gaza cika alkawurran da ka dauka.
"Mafi yawancin yan Najeriya suna hawa mulki ne ba tare da suna da wata tsari ba shi yasa idan sun hau kuma lamura ba su tafi yadda ya kamata ba sai suyi ta kuka da na bayansu," inji Gwarzo.
Mataimakin Atiku na musamman kan matasa da tsare tsare, Dr Ahmed Adamu ya ce, "Yau komai ya koma yanar gizo. Shima zaben yana komawa yanar gizo. Idan kai dan siyasa ne ko mai fada aji hanyar da ta fi dace wa ka watsa sakonnin ka shine ta yanar gizo.
Ya kara da cewa "akwai kimanin yan Najeriya miliyan 130 da ke amfani da yanar gizo wannan adadin ya kai wadanda za su iya zaben shugaban kasa. Atiku yana da tsari mai kyau ga yan Najeriya. Matsalarsa shine yadda zai isar da sakonsa ga yan Najeriya."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng