Da duminsa: Kotu a jihar Kano ta sake yanke wa wani hukuncin kisa

Da duminsa: Kotu a jihar Kano ta sake yanke wa wani hukuncin kisa

Wata kotun Musulunci da ke zama a jihar Kano ta yanke wa wani tsoho hukuncin kisa ta hanyar jifa sakamakon laifin yi wa karamar yarinya fyade da aka kama shi da shi.

Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, alkalin kotun, ya ce za a kashe tsohon mai suna Mati Audu ta hanyar jifa.

Kotun ta samu Mati Audu mai shekaru 70 da laifin yi wa wata karamar yarinya mai shekaru 12 fyade a karamar hukumar Tsanyawa.

Tsoho Mati Audu ya tabbatar wa da kotun cewa shi ya aikata laifin fyaden. An dage shari'ar har sau hudu inda alkalin ya ba shi dama ko zai sauya ra'ayinsa da shaidarsa.

Amma kuma, a kowanne karo da aka koma zaman kotun, ya jaddada cewa shi ya yi wa karamar yarinyar fyade inda ya bukaci a yafe masa.

Bayan nan, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola ya karanto sassan Al-Kur'ani mai tsarki da kuma wasu hadisan Manzon Allah wadanda suka nuna girman laifin da Mati Audu ya aikata.

Daga nan ya yanke hukuncin kisa ta hanyara jifa kamar yadda sashi na 127 na kundin tsarin shari'ar Musulunci na jihar Kano ta bayyana.

Matsalar fyade na neman zama ruwan dare a fadin Najeriya ba jihar Kano kadai ba. Lamarin da yasa wasu ke gani ya kamata a dauka tsauraran mataki a kan masu aikata laifin.

Da duminsa: Kotu a jihar Kano ta sake yanke wa wani hukuncin kisa
Da duminsa: Kotu a jihar Kano ta sake yanke wa wani hukuncin kisa. Hoto daga The Nation
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Hukuncin kisa a kan matashin Kano: Tijjaniya ta yi martani a karon farko

Idan za mu tuna, wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan wani matashi mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukuci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, a yau, Litinin.

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

An gurfanar da matashin mawaki Yahaya a gaban kotu bayan an zargeshi da wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga annabi Muhammad a cikin watan Maris na shekarar 2020.

Bayan wallafa wakar da kuma yaduwarta a dandalin sada zumunta, musamman Whatsapp, wasu fusatattun matasa sun kone gidan su matashin tare da jagorantar zangaz-zanga zuwa hedikwatar hukumar Hisbah.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel