Hukuncin kisa a kan matashin Kano: Tijjaniya ta yi martani a karon farko

Hukuncin kisa a kan matashin Kano: Tijjaniya ta yi martani a karon farko

Kungiyar Tijjaniyya ta barranta kanta da Yahaya Shariff Aminu, matashin jihar Kano da aka yanke wa hukuncin kisa a Kano bayan kama shi da laifin batanci da aka yi ga Annabi Muhammadu.

Wannan ne lokaci na farko da manyan kungiyoyin addini na kasar Najeriya suka yi martani a kan wannan hukuncin da aka yanke a ranar Litinin.

Shugaban majalisar zawiyoyin Tijjani da ke Kano, Mallam Muhammad Nura Arzai, ya sanar da BBC cewa, ko kadan abin da matashin ya aiwatar ba sa cikin ladubba da koyarwar Sheikh Ibrahim Inyass.

"Mu almajiran Shehu Inyas, muna farin cikin wannan hukuncin kisan da aka yanke wa wanda ya taba martabar fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu S. A. W," cewar Muhammad Nura Arzai.

Idan za mu tuna, wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan wani matashi mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukuci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, a yau, Litinin.

KU KARANTA: Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

An gurfanar da matashin mawaki Yahaya a gaban kotu bayan an zargeshi da wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga annabi Muhammad a cikin watan Maris na shekarar 2020.

Bayan wallafa wakar da kuma yaduwarta a dandalin sada zumunta, musamman Whatsapp, wasu fusatattun matasa sun kone gidan su matashin tare da jagorantar zangaz-zanga zuwa hedikwatar hukumar Hisbah.

A cewar rahoton jaridar 'Focus' da Daily Nigerian ta kara yadawa, kotun ta zaratar da hukuncin daurin shekaru 10 a kan wani matashi mai suna Umar Farouq sakamakon furta kalaman raini a kan Allah.

An gurfanar da Farouq a gaban kotun ne bisa tuhumarsa da furta kalaman raini ga Allah yayin musu da abokansa a unguwar Sharada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel