Zulum ya mayar da mutum 560 gida bayan harin Auno

Zulum ya mayar da mutum 560 gida bayan harin Auno

Gwamna Babagana Zulum ya mayar da mutum 560 da suka bar yankin Auno ta karamar hukumar Konduga ta jihar bayan watanni shida da suka bar garin saboda mayakan Boko Haram.

Mustapha Gubio, kwamishinan gyara na jihar, ya sanar da hakan a taron manema labarai da yayi a Maiduguri a ranar Talata.

Gubio ya tunatar da yadda mazauna yankin suka bar gidajensu a ranar 9 ga watan Fabrairu bayan harin da 'yan bindigar suka kai yankin. Sun kashe mutum 8 tare da tarwatsa kadarorin miliyoyin Naira.

Ya ce mutanen da suka dawo gida sun samu mafaka ne a Njimtilo, Jakana, Malam Karamti da Malam bukarti da ke Konduga, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan ya kara da cewa, Gwamna Zulum, ya samu wasu kudi daga bankin masana'antu, wanda da su yayi amfani ya gina sabbin gidaje 80 don 'yan gudun hijira a Auno.

Kamar yadda yace, gwamnatin jihar na kokarin gina wasu karin gidaje 100 daga kudin don amfanin 'yan gudun hijirar.

"Gwamnatin jihar ta duba yadda aikin gina wurin koyon sana'a, wanda gidauniyar Alhaji Muhammadu Indimi ta dauka nauyi ke tafiya a garin Auno.

Zulum ya mayar da mutum 560 gida bayan harin Auno
Zulum ya mayar da mutum 560 gida bayan harin Auno. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed

“Aikin idan aka kammala zai samar da wurin sana'a da za a inganta rayuwar mutanen yankin," yace.

Hakazalika, Dr Mairo Mandara, mai bai wa gwamna shawara a kan walwala da jin kan 'yan jihar, ta jaddada kokarin ganin tabbatar da wasu tsari da shirye-shirye don samar da mafita ga matasa da mata.

Mandara ta yi kira ga jama'ar da suka dawo gida da su dage da neman na kansu ta hanyar mayar da hankali a noma da kiwo.

A bangarenta, Yabawa Kolo, shugabar hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA), ta ce 'yan gudun hijirar da kansu suka yanke hukuncin komawa gida don komawa rayuwarsu.

Kolo ta ce hukumar ta raba kayan abinci da ababen bukata don rage radadi ga dukkan wadanda suka dawo gida. Kayan da aka raba sun hada da shinkafa, man gyada, gidan sauro, bargo, sutura da katifu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel