Shirin NPower da ciyar da dalibai: Idan ba mutum mai imani irin Buhari ba, babu wanda zai iya - Badaru

Shirin NPower da ciyar da dalibai: Idan ba mutum mai imani irin Buhari ba, babu wanda zai iya - Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, ya bayyana cewa babu shirin walwala da jin dadin mutanen da yafi na gwamnatin shugaba Buhari a duniya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Laraba a garin Gagarawa yayinda yake kaddamar farawan shirin a kananan hukumomin jihar 18, The Sun ta ruwaito.

"Ban taba ganin irin shirin jin dadin al'umma mai girma, kuma ya game kowa irin wannan a fadin duniya ba" Badaru Talamiz ya laburta.

"Aiwatar da irin wannan mutum mai imani ne kawai zai iya zuba kudi mai yawa hannun talakawa."

Ya ce masu sukar gwamnatin nan wasu yan tsiraru ne masu hali da basu ki gwamnatin ta rushe ba don su cigaba da cin rashawansu.

Badaru ya ce jiharsa ne aka fi yawan adadin masu amfana da shirin, inda aka biya mutane 26,734 tsakanin Agustan 2017 da Afrilun 2020.

KU KARANTA: Mu shugabancin kasa muke so a 2023 ba Biyafara ba - Ohanaeze Ndigbo

Bayan kashe bilyan 9 kan ciyar da dalibai da N-Power, Badaru yace babu irin Buhari a duniya
Badaru
Asali: Depositphotos

Cikin kimanin shekaru 4, gwamnatin tarayya ta kashe Bilyan 14 kan shirye-shiryen ma'aikatar walwala da jin dadin al'umma dake karkashin Hajiya Sadiya Umar Farouq a jihar Jigawa kadai.

Shirye-shiryen sun hada da ciyar da daliban makarantar Firamare, shirin N-Power na matasa, da shirin rabawa marasa karfi kyautan dubu biyar kowani wata.

Yayinda aka kashe N9.074bn kan shirin dubu biyar-biyar da ake ba marasa karfi a wata, an kashe Bilyan 5.178 kan shirin ciyar da daliban makarantar Firamare daga shekarar 2017 zuwa yanzu a Jigawa.

Jagoran shirin na jihar Jigawa, Bala Chamo, wanda ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Dutse ranar Asabar ya ce an kashe bilyan N9.074 a kananan hukumomi tara, Premium Time ta dauko.

Chamo ya ce komai a shirye yake domin biyan sabbin matasan N-Power da aka dauka na sauran kananan hukumomi 18 a jihar.

Ya ce sabbin daukan su saurari jn kararrwar bankin na kudinsu daga ranar Talata, 11 ga Agusta, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel