Ministan Harkokin Waje ya warke daga cutar korona

Ministan Harkokin Waje ya warke daga cutar korona

Ministan harkokin wajen Najeriya, Mista Geoffery Onyeama, ya warke sumul daga cutar korona.

Idan ba a manta ba ministan ya kamu da kwayoyin cutar a watan Yulin da ya gabata bayan da ya nemi jin ba’asin kaikayin makwagoro da ya addabe shi.

A yanzu ministan ya wartsake sumul inda a ranar Laraba, 12 ga watan Agusta, ya sanar da wannan albishir ga mabiyansa a dandalin sada zumunta na Twitter.

Mista Onyeama ya tsarkaka daga kwayoyin cutar korona bayan ya shafe kimanin makonni uku a killace.

Ministan Harkokin Waje; Geoffery Onyeama
Hoto daga jaridar Pulse
Ministan Harkokin Waje; Geoffery Onyeama Hoto daga jaridar Pulse
Asali: Twitter

A cikin sakon da ministan ya wallafa, ya yi godiya gami da jinjina ga kwararrun lafiya da suka yi jinyarsa, ‘yan uwa, makusanta, abokanan aiki da dukkan wadanda suka yi masa fatan alheri.

Ya ce: “kulawarku, addu’o’i, da sakonninku na goyon baya, sun yi tasiri wajen samun waraka da kasancewa mai koshin lafiya da nake cikinta a yanzu.”

A halin yanzu dai adadin mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun kai 47,290 tun bayan da cutar ta bulla karo na farko a watan Fabrairu.

Hakan yana kunshe cikin kididdigar alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC ta sanar a ranar Talata da daddare.

KARANTA KUMA: Tsarin IPPIS baƙon abu ne da ba zai karbu ba a Najeriya - ASUU

Alkaluman hukumar NCDC sun nuna cewa, a yayin da mutum 33,609 sun samu waraka, 956 kuma sun riga mu gidan gaskiya.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 319,851 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 12,725 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

A cikin sanarwar da NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce an gano sabbin mutane 423 da suka kamu a jihohin Najeriya 22 kamar haka:

Lagos (117), Abuja (40), Ondo (35), Rivers (28), Osun (24), Benue (21), Abia (19), Ogun (19), Ebonyi (18), Delta (17), Kwara (17), Kaduna (15), Anambra (14), Ekiti (11), Kano (9), Imo (6), Gombe (4), Oyo (3), Taraba (3), Bauchi (1), Edo (1) da Nasarawa (1).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel