Rayuka sun salwanta yayinda 'yan Boko Haram suka kai sabon hari jihar Borno

Rayuka sun salwanta yayinda 'yan Boko Haram suka kai sabon hari jihar Borno

Kimanin manoma da makiyaya 13 ake tsoron sun rasa rayukansu yayinda yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suka kai farmaki garin Puciwa da Koleram dake karamar hukumar Magumeri a jihar Borno.

Sakataren karamar hukumar, Mallam Wali, ya tabbatarwa The Guardian da yammacin Litnin cewa yan ta'addan sun jikkata mutane 16 kuma sun yi awon gaba da shanaye, tinkiyoyi da akuyoyi.

Sakataren ya ce garin Gubio da garin Gajiram dake makwabtaka da Magumeri sun kasance karkashin yan ta'addan.

"Yan ta'addan sun dira garuruwan biyu da yammacin (Litinin). Sun yi awon gaba da shanaye, tinkiyoyi da akuyoyi. Sun jikkata mutane 16 bayan 13 da suka kashe." Yace

"Kimanin sa'a daya bayan harin, mutanennmu suka gudu Magumeri, kimanin Kilomita 40 da Maiduguri, babbar birnin jihar."

"Gaba daya al'ummar Gubio da Gajiram dake da iyaka da karamar hukumar Nganzai na fuskantar hare-hare daga yan ta'addan kullum."

Ya bayyana cewa mutan kauyen sun shiga cikin halin kakanikaye saboda yan ta'addan sun rarike musu dukiya.

"Amma muna iyakan kokarinmu wajen kula da yan gudun hijra," Mallam Wali ya laburta.

Rayuka sun salwanta yayinda 'yan Boko Haram suka kai sabon hari jihar Borno
Rayuka sun salwanta yayinda 'yan Boko Haram suka kai sabon hari jihar Borno
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Tsohin Sarkin Kano, Sanusi Lamido, zai koma makaranta

A bangare guda, Hukumar tsaron farin kaya DSS ta sammaci tsohon mataimakin gwamnan bankin CBN, Obadiah Mailafiya.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an sammaceshi ne kan jawabin da yayi inda ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da aka saki ya fada masa cewa wani gwamnan Arewa ne shugaban yan Boko Haram.

Dr Obadiah Mailafia ya ce shi da wasu masu ruwa da tsaki a yankin sun tattauna da tubabbun yan bindiga kuma sun fada musu daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.

Mailafia ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Nigeria Info FM a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2O2O.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel