INEC ta saka ranar yin zabukan maye gurbi 12 a fadin kasar nan

INEC ta saka ranar yin zabukan maye gurbi 12 a fadin kasar nan

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta saka ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar yin zaben maye gurbi na 'yan majalisaun tarayya da na jihohi.

Bayelsa ta tsakiya, Bayelsa ta kudu, Cross River ta arewa, Imo ta arewa, Legas ta gabas da Flato ta kudu duk mazabu ne da basu da 'yan majalisa a majalisar dattawa.

Douye Diri da Lawrence Ewhrudjakpo, sanatoci ne da suke wakiltar mazabun Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta kudu, kuma aka zabesu a matsayin gwamna da mataimakinsa na jihar Beyelsa.

Sanatoci masu wakiltar Cross River ta arewa, Imo ta arewa, Legas ta gabas da Filato ta kudu duk rasuwa suka yi.

A wata takarda da Festus Okoye, kwamishinan yada labarai na INEC ya fitar a ranar Talata, ya ce hukumar ta dakatar da dukkan zabukan maye gurbi ne saboda annobar korona.

Okoye ya ce hukumar ta habaka yadda za ta dinga yin zabukanta duk da annobar korona da ta addabi kasar nan.

INEC ta saka ranar yin zabukan maye gurbi 12 a fadin kasar nan
INEC ta saka ranar yin zabukan maye gurbi 12 a fadin kasar nan. Hoto daga Punch
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Da duminsa: Kano ta nada sabbin alkalai 6 na babbar kotu (Sunaye)

"An samu gurabe masu tarin yawa a majalisun tarayya da na jihohi saboda murabus ko mutuwar mambobin. Hakan ya shafi mazabu 12 a cikin jihohi 8 na kasar nan.

“Hukumar ta yi nasarar yin zaben mazabar jihar Nasarawa ta tsakiya na jihar kuma tana ci gaba da shirin zaben Edo da Ondo a ranar 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba," yace.

Jerin zabukan da za a aiwatar na maye gurbi suna hada da:

1. Kujerar sanata ta jihar Bayelsa ta tsakiya.

2. Kujerar sanata ta jihar Bayelsa ta kudu.

3. Mazabar Nganzai a jihar Borno ta tarayya.

4. Mazabar Bayo ta tsakiya, a jihar Borno.

5. Kujerar sanat ta Cross River ta arewa.

6. Mazabar Obudu ta jihar Cross River.

7. Kujerar sanata ta Imo ta arewa.

8. Kujerar sanata ta jihar Legas ta gabas.

9. Mazabar Kosofe II da ke jihar Legas.

10. Kujerar sanata da jihar Filato ta kudu.

11. Mazabar Bakura ta jihar Zamfara.

12. Mazabar Ibaji ta jihar Kogi.

“Hukumar ta saka ranar Asabar, 31 ga watan Oktoban 2020 a matsayin ranar yin dukkan zabukan maye gurbin."

Kwamishinan ya ce, jam'iyyun siyasa za su yi zaben fidda gwani tsakanin ranar 24 ga watan Augusta zuwa 8 ga watan Satumba.

"Za a kai wa INEC fom da kuma takardun 'yan takara daga ranar 9 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Satumban 2020," yace.

Kwamishinan ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da jam'iyyun siyasa da su kiyaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel