Binciken Magu: Sagay ya soki Kwamitin Mai Shari'a Salami

Binciken Magu: Sagay ya soki Kwamitin Mai Shari'a Salami

Shugaban kwamitin masu ba shugaban kasa shawara kan harkokin cin hanci da rashawa, Itse Sagay, ya tofa albarkacin bakinsa kan irin salon bincike da ake yi wa Ibrahim Magu.

A ranar Litinin, 10 ga watan Agusta, Farfesa Sagay ya kausasa harsashen kan abin da ya misalta a matsayin rashin dangane da tsarin gudanar da binciken kan zargin almundahana da ake yi wa Magu.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Sagay ya bayyana rashin gamsuwa da yanayin mutanen da aka saka a matsayin Mambobin Kwamitin binciken Magu wanda Mai Shari’a Ayo Salami yake jagoranta.

Farfesa Itse Sagay
Farfesa Itse Sagay
Asali: UGC

Sagay ya nuna bacin rai a kan yadda kwamitin ke kiran masu zargin Magu a bayan idon sa, kuma a hana shi sanin bayanan tuhuma da su gabatar a kanshi, wanda da su zai yi amfani wajen shirin kare kan sa a gaban kwamitin binciken.

A cewar Farfesa Sagay, wanda kwararren lauya ne kuma masanin shari’a, ya ce Mai Shari’a Salami ne kadai ya ke aiwatar da abin da ya dace wajen binciken Magu ba tare da wani ra’ayi na daban ba.

Sagay ya ce, “a bisa dukkan alamu, duk cikin ‘yan kwamitin kakaf din su Mai Shari’a Ayo Salami ne kadai adali a cikin su, wanda kuma ba wata boyayyar manufa da ya ke karewa face gano gaskiya.”

KARANTA KUMA: Trump ya turo da agajin na'urar taimakon numfashi 200 zuwa Najeriya

Daga cikin 'yan kwamitin masu binciken Magu da ya kunshi mutum bakwai sun hadar da; Tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara; Mai Shari'a Ayo Salami da Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Michael Ogbezi.

Sauran sun hadar da Wakilin Ma'aikatar Shari'a ta Tarayya, Muhammad Babadoko, da Wakilin Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS), Hassan Abdullahi.

Akwai kuma Muhammad Shamsuddeen daga Ofishin Akanta Janar, Douglas Egweme daga cibiyar binciken harkallar Kudi da kuma Kazeem Atitebits a matsayin sakataren kwamitin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: