Trump ya turo da agajin na'urar taimakon numfashi 200 zuwa Najeriya

Trump ya turo da agajin na'urar taimakon numfashi 200 zuwa Najeriya

Daga karshe, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya aiko da agajin na’urar taimakawa numfashi 200 da ya yi wa Najeriya alkawari tun da dadewa.

Cikin wata tattaunawa da ya yi ta hanyar wayar tarho tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari tun a watan Afrilun da ya gabata, Trump ya yi alkawarin tallafawa Najeriya da na’urar taimakawa numfashi.

Shugaban Amurka ya yi wannan alkawari domin kara wa Najeriya kwarin gwiwar yaki da annobar korona kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sai dai a yanzu bayan kusan watanni biyar, Shugaban na Amurka ya sauke nauyin kayan alkawari da dauka ta hanyar cika shi.

Ministan Lafiya; Osagie Ehanire
Ministan Lafiya; Osagie Ehanire
Asali: UGC

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, shi ne ya karbi na’urorin taimakawa numfashi 200 a madadin gwamnatin tarayya ranar Talata a hannun Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID.

Mista Ehanire cikin jawaban da ya yi a birnin Abuja, ya ce na’urorin na da muhimmancin gaske ta yadda za su taka rawar gani wajen tseratar da rayuwar mutanen masu fama da matsananciyar cutar korona.

Ministan ya kara da cewa, tabbas yanayi na rayuwar al’ummar Najeriya ya sauya tun yayin da a watan Fabrairu aka samu bullar cutar korona karo na farko a kasar.

Tuni Najeriya ta fara shirin karbar na'urorin taimakon numfashi guda 200 da gwamnatin Amurka ta yi alkawarin bayar da gudunmuwa.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammad, inda da zarar na'urorin sun iso za a sanar wa al'umma.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Hukumar takaita yaduwar Cututtuka a Najeriya NCDC, ta bayyana cewa cutar korona ta sake harbin sabbin mutane 423 a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Zaben Ondo: APC ta nada Sanwo Olu shugaban kwamitin yakin neman zabe

Hukumar NCDC a sanarwar da ta fitar a da misalin karfe 11:20 na daren ranar Talata 11 ga Agusta, ta ce an gano sake gano karin mutum 432 da masu dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar.

Sabbin mutum 423 da suka kamu a jihohi 22 sun kasance kamar haka: Lagos (117), Abuja (40), Ondo (35), Rivers (28), Osun (24), Benue (21), Abia (19), Ogun (19), Ebonyi (18), Delta (17) da Kwara (17).

Sai kuma Kaduna (15), Anambra (14), Ekiti (11), Kano (9), Imo (6), Gombe (4), Oyo (3), Taraba (3), Bauchi (1), Edo (1) da Nasarawa (1)

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel