Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed

Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya nada wata hukuma domin bincikar yanayin da aka bi domin siyar da kadarorin jihar Kwara karkashin gwamnoni Muhammad Lawal, Bukola Saraki da Abdulfatah Ahmed.

Gwamnan ya nada wani kwamitin domin bincikar wani zargin waskar da kudade har naira miliyan 300 na kananan hukumomi da aka yi a karkashin mulkin sa.

A yayin da aka bai wa hukumar wa'adin watanni biyu don kawo rahotonta, kwamitin bincike a kan kudaden kananan hukumomi an ba shi makonni biyu don kawo sakamakonsa.

A yayin kaddamar da kwamitocin, gwamnan ya ce tuni hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta fara aikin bincike a kan kudaden kananan hukumomi da kuma yadda aka rarraba su, bayan goron gayyata da ya ba su.

A wata takarda da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar, ya ce gwamnan tun a ranar 14 ga watan Yulin ya bukaci EFCC da ta duba yadda aka rarraba kudin ga kananan hukumomi 16, da kuma kudin shiga da aka samu don tabbatar da cewa babu kudin da aka waskar.

Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed
Gwamna Abdulrazak ya rantsar da kwamitin bincike kan mulkin Lawal, Saraki da Ahmed. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Dole in mayar da Obasanjo gidan fursuna idan na hau shugabancin kasa - Fayose

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, da ya yi amfani da kujerarsa wurin assasa hadin kai na yankin arewacin kasar nan.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne ga sarkin yayin da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar a ranar sati, kamar yadda yake kunshe a wata takarda da mai bada shawara na musamman a kan fannin yada labarai ga gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar.

Matawalle ya jaddada cewa arewa na matukar bukatar shugabanni da za su hada kan jama'a don komawa saiti daya na siyasa da al'adu.

"Mai martaba, arewa na bukatar shugabanninsu da za su hada kan jama'arta a siyasance da al'adance kamar baya," Matawalle ya ce.

Gwamnan ya danganta rashin hadin kan yankin da ci gaban rashin ganin girman sarakunan gargajiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: