Rudani: An samu bam a tsakiyar wata babbar kasuwar Najeriya

Rudani: An samu bam a tsakiyar wata babbar kasuwar Najeriya

Rikici da rudani sun barke a babbar kasuwar Ophoke-Abba, da ke Kpiri-Kpiri a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a ranar Litinin da yammaci.

Hakan ta faru ne kuwa bayan an samu wani abu da ake zargin bam ne a kasuwar, jaridar The Nation ta wallafa.

Gano bam din ya ruda 'yan kasuwa, masu siyayya da kuma masu wucewa inda suka dinga gudu don tseratar da rayuwarsu.

Lamarin da ya faru wurin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, ya sa 'yan kasuwar sun tashi babu niyya tun kafin karfe 6 na yammaci da suka saba tashi.

Wani dan kasuwa mai suna Paul Onwe, wanda ya zanta da manema labarai ya ce lamarin ya faru tamkar yaki.

"Babu zato balle tsammani jama'a suka fara gudu tare da ihun bam, bam, bam. Suna cewa na dasa bam a kasuwar.

"A cikin sakanni, labarin ya karade kasuwar kuma mutane sun fara gudu dutse a hannun riga yayin da kananan yara ke ta kuka.

Rudani: An samu bam a tsakiyar wata babbar kasuwar Najeriya
Rudani: An samu bam a tsakiyar wata babbar kasuwar Najeriya. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dole in mayar da Obasanjo gidan fursuna idan na hau shugabancin kasa - Fayose

“Na yi kokarin kwashe kayana, rufe shagona sannan na tsere na bar kasuwar. Ban taba ganin irin wannan abu ba a dukkan rayuwata," Onwe yace.

Wata ganau ba jiyau ba mai suna Edith Agu, ta ce labarin cewa an dasa bam a tsakiyar kasuwar nan da nan ya karade ta kuma mutane sun fara neman wurin buya.

Agu ta ce da gaggawa ta kwashe kayanta sannan ta bar kasuwar baki daya, ta kara da cewa lamarin ya katse hanzarin kasuwanci a kasuwar baki daya.

Agu ta ce labarin bam ya tada hankalin jama'a ta yadda da yawansu suka bar kayayyakinsu suka tsere suka bar kayansu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta ce an kira 'yan sanda masu cire bam don dauke shi amma ba za ta iya cewa ga sashin da aka sameshi ba a kasuwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel