Covid-19: Badaru ya rarraba kayan abinci ga magidanta 40,000 a Jigawa

Covid-19: Badaru ya rarraba kayan abinci ga magidanta 40,000 a Jigawa

A ranar Talata, 11 ga watan Agusta, gwamnatin jihar Jigawa ta fara rarraba kayayyakin jin kai ga marasa galihu 42,312 da ke fama da rauni a jihar.

Haka kuma gwamnatin ta sanar da cewa an shafe tsawon kwanaki 23 ba tare da samun wanda cutar korona ta harba ba a cikin jihar.

Gwamnan Muhammad Badaru, shi ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da shirin rarraba kayayyakin jin kai wanda hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu da ke yaki da cutar korona suka bayar da gudunmuwa.

Cikin jawaban da ya gabatar a Dutse, babban birnin Jihar, Gwamna Badaru ya ce magidanta 12 ne daga kowace mazaba ake tsammanin za su ci moriyar wannan kayayyaki na tallafi.

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru
Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru
Asali: Twitter

“A kokarin da muke yi na tabbatar da cewa dukkan magidantan da suka cancanta sun samu wani kaso na tallafi, mun yanke shawarar rarraba kayayyakin a dukkan mazabu 3,526 da jihar ta kunsa.”

“A kowace mazaba daya, magidanta 12 za su ci moriya, amma duk da hakan kowace karamar hukuma za ta samu na ta kasafin gwargwadon adadin mazabu da ta kunsa,” Gwamnan yake cewa.

“Wannan na nufin magidanta 42,312 za su ci moriyar kayayyakin tallafin a dukkan mazabu da ke sassan jihar.” Yace

KARANTA KUMA: Gwamna Lalung ya bayyana damuwa kan yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ya yi kamari a Filato

Yayin karin haske dangane da matakin yaki da cutar korona a jihar, gwamnan ya ce: “a yau mun cika kwanaki 23 ba tare da samun wanda cutar korona ta harba ba a jihar.”

“A yayin da wannan dalili ne da zai sa mu yi farin ciki, amma abu mafi muhimmanci shi ne mu yi wa Allah godiya da ya kawo mana sauki cikin al’amuran da sannu a hankali muke ganin karshen wannan annoba.”

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, daga cikin kayayyakin tallafi da za a rarrabawa kowane magidanci da ya cancanta a jihar sun hadar da buhun shinkafa, kwalin taliya, buhun sukari, da buhun gishiri.

Sauran sun hadar da; kwalin taliyar yara, buhun garin rogo, buhun garin tuwo da kuma buhu masara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel