Lauya ya koka da kazantaccen muhallin 'yan sandan Najeriya (Hotuna)

Lauya ya koka da kazantaccen muhallin 'yan sandan Najeriya (Hotuna)

- Fitaccen lauya mai suna Liborous Oshoma, ya koka da halin da barikin 'yan sandan Najeriya ke ciki domin ya danganta hakan da kuntata wa jami'an

- Oshoma ya kara da cewa, mummunan halin da ma'aikatan ke ciki a gidajensu bai dace da tunanin da kuma kwanciyar hankalin 'yan sandan ba

- Lauyan ya tuhumi yadda ake kasafin kudi kuma da inda suke zuwa domin kuwa 'yan Najeriya ne za su fi shan wahala a kan abinda ke faruwa

Wani fitaccen lauya mai suna Liborous Oshoma, ya jajanta halin da 'yan sandan Najeriya ke ciki a yayin da ya wallafa munanan hotunan halin da barikinsu ke ciki.

A shafinsa na Instagram a ranar Litinin, 10 ga watan Augusta, masanin shari'ar ya ce saboda kare mutuncin aikinsu, dole ne a kare musu bukatunsu don samun biyan bukatar 'yan Najeriya wurin samun kariya.

Oshoma ya kara da cewa, lalacewar bangaren ba a rana daya bane. Ya ce hakan ya faru ne sakamakon halin ko in kula da gwamnatoci suka bayyana ga bangaren.

KU KARANTA: Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)

Ya ce halin da hukumar ke ciki na sa a dinga yin tambayar anya ana ware wa hukumar kudi kuwa na gyaran barikinsu. Lauyan ya kara da tambayar cewa, mai yasa masu wawure wadannan kudaden basu fuskantar fushin hukuma?

Lauya ya koka da kazantaccen muhallin 'yan sandan Najeriya (Hotuna)
Lauya ya koka da kazantaccen muhallin 'yan sandan Najeriya (Hotuna). Hoto daga Oshoma
Asali: UGC

Oshoma ya ce tunda 'yan sandan ba za su iya jure wa wannan rashin walwalar da kula daga gwamnati ba, tabbas talakawa ne za su fuskanci abinda zai je ya dawo.

Kamar yadda wani sashi na wallafar ya bayyana: "Wannan bai faru a dare daya ba, ya kai ga haka ne bayan tsawon shekaru da aka dauka ana yi wa 'yan sandan, tare da rashin mutunta kayayyakin gwamnati.

"Daya daga cikin abubuwan da ke damuna kuma nake son tamabaya shine, akwai wani kasafin kudi kuwa da ake warewa duk shekara don gyaran barikin 'yan sandan?"

A wani labari na daban, Legit.ng ta wallafa cewa sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya kaddamar da shirin ciyarwa tare da tallafi ga 'yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel