Dole in mayar da Obasanjo gidan fursuna idan na hau shugabancin kasa - Fayose
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya sha alwashin mayar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zuwa gidan fursuna a kan manyan laifukan da ake zarginsa da su.
Fayose ya ce zai tabbatar da cewa Obasanjo ya bada bayani dalla-dalla a kan wasu laifukan rashawa da ake zarginsa da su a shekaru takwas da ya kwashe yana mulkin kasar nan, sannan kuma ya fuskanci fushin hukuma.
Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da aka zanta da shi a wani shirin siyasa da ake yi a gidan talabijin na PlusTV Africa, wanda jaridar The Nation ke yi a Ado Ekiti.
Tsohon gwamnan da Obasanjo suna sukar juna ne tun bayan da Obasanjo ya fitar da wasikar ta'aziyyar Sanata Buruji Kashamu.
A wasikar ta'aziyyar da Obasanjo ya aika wa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya zargi Kashamu da amfani da shari'a da siyasa wurin gujewa shari'a amma ya kasa gujewa mutuwa.
Amma kuma, a ta'aziyyar Fayose, ya kwatanta wasikar tsohon shugaban kasar da abun takaici tare da cewa "'Yan Najeriya na jiran ganin yadda za ka kare kai ma".
KU KARANTA: Ka yi amfani da kujerarka wurin kawo hadin kai a arewa - Matawalle ga Sarkin Kano
A yayin martani ga Fayose, Obasanjo ya ce jama'a na iya makoki a duk yadda suka so bayan mutuwarsa. Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su duba tsokacinsa na mutuwar Kashamu ta yadda za su yi rayuwa mai amfani.
Amma kuma, Fayose ya yi martani inda ya ce tsohon shugaban kasar ya kamata ya fuskanci hukunci a kan miyagun maganganun da yayi a kan marigayi Kashamu.
"Bari in sanar da kai, Obasanjo ya yi furucin kiyayya kuma kamata yayi gwamnati ta dauka mataki.
"Ina fatan wata rana zan zama shugaban kasa. Obsanjo zai koma gidan yari. Ina sanar da ku gaskiya saboda akwai abubuwa da yawa da ya kamata a tuhumi Obasanjo a kai.
"Obasanjo ba waliyyi bane. A lokacin da ya fito daga gidan yari, gonarsa ta Ota ta tagayyara. Ta ina ya samo kudin farfado da ita? Daga gwamnati ne.
"A kan dakin karatu, gwamnoni a wancan lokacin sun bada gudumawar N10 miliyan don goyon bayan Obasanjo ta dole. Tazarce na uku har yau yana nan a kwakwalwarmu. Obasanjo ba waliyyi bane," ya kara da cewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng