Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"

Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"

Shugaba Muhammadu Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da ke yankin arewa maso gabashin kasar a matsayin mayunwata da ke neman abinci da za su ci.

Da ya ke magana yayin taron da ake gudanar da fadar shugaban kasa a ranar Talata, Buhari ya ce shugabannin hukumomin tsaron sun yi iya kokarinsu amma akwai bukatar su kara kaimi a bangaren tattara bayannan sirri.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugabannin rundunar sojoji, hukumomin tattara bayanan sirri da mambobin kwamitocin tsaro da wakilan kungiyar gwamnonin Najeriya sun hallarci taron.

Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci"
Buhari ya kwatanta mayakan Boko Haram da "mayunwata masu nema abinci". Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Gabriel Olonisakin, shugaban hafsoshin tsaro; Tukur Buratai, shugaban sojojin kasa; Sadique Abubakar, shugaban sojojin sama, da Ibok-Ete Ekwe Ibas, shugaban sojojin ruwa, duk sun hallarci taron.

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Shugaban kasar ya bayyana damuwarsa a kan yadda yan taaddan ke samun kananan makamai duk da rufe iyakokin kasa da aka yi.

"Yan taadan suna nan a cikin kasar nan. Ta yaya har yanzu suke samun kananan makamai? kamar yadda kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya jiyo shugaban ta tambayan shugabanin tsaron.

"Ina farin ciki domin akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro. Na umurci shugabanin tsaron su rika ganawa da juna kafin taron Kwamitin Tsaro ta Kasa.

"Hukumomin tsaron mu suna da kayan aiki; duk da cewa suna bukatar kari amma dai suna iya kokarin su akwai bukatar inganta tattara bayanan sirri da fassara ta.

Da ya ke karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa yan taadan sun fi sojoji makamai, an ruwaito shugaban kasar ya ce abinda ya yi saura cikinsu: "mayunwata ne masu farautar abinda za su ci, suna sata a shaguna, kasuwanni suna kashe mutanen yayin hakan."

Buhari ya sanar da gwamnoni cewa akwai wasu makamai da jirgagen yaki da aka yi oda daga Jordan, China da Amurka amma ya kara da cewa sai anyi hakuri saboda ana bukatar kwararrun matukan jirgin yaki da za suyi amfani da sabbin makaman da jiragen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel