DSS ta kama wani da ke damfara da sunan shugaban ma'aikatan fadar Buhari

DSS ta kama wani da ke damfara da sunan shugaban ma'aikatan fadar Buhari

Hukumar Yan Sandan Farar Hula DSS ta kama wani Mohammed Prince Momoh, 42, kan zarginsa da yin amfani da sunan shugaban ma'aikatan fadar Buhari, Ibrahim Gambari don damfarar wani Benson Aniogo, $50, 000.

Kakakin DSS, Peter Afunanya ya ce Momoh ya yi yunkurin damfarar Aniogu bayan ya yi ikirarin shi wakilin Gambari ne kuma yana bukatar kudin don ya sa a nada shi makamin mashawarcin Shugaban kasa na musamman kan Man fetur da iskar Gas.

Afunanya ya ce wanda ake zargin, dan asalin jihar Kogi, ya tuntubi Aniogu dan jihar Bayelsa inda ya fada masa cewa shi mai tsaron Gambari ne.

DSS ta kama wani da ke damfara da sunan shugaban maaikatan fadar Buhari
DSS ta kama wani da ke damfara da sunan shugaban maaikatan fadar Buhari. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Momoh ya yi ikirarin cewa za a bawa Gambari $25, 000 yayin da sauran kudin kuma za a raba wa wadanda za su taimaka lamarin ya yi wu a nada shi mukamin.

DUBA WANNAN: Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Afunanya ya ce Momoh ya yi aiki na kankanin lokaci a baya a fadar shugaban kasa kuma yasa yadda wasu harkoki ke tafiya a can. Ya ce Momoh da tawagarsa sun ziyarci Aniogu da gidansa da ke Abuja domin karbar kudin.

Amma sai wanda abin ya faru da shi nan take ya yi zargin kamar 'yan damfara ne kuma ya sanar da jami'an tsaro kuma nan take suka saka aka kama Momoh.

Kakakin na DSS, ya shawarci yan Najeriya da ke amfani da dandalin sada zumunta su yi takatsantsan da bata gari da ke sace bayannan su suyi amfani da su wurin damfara.

"Su rike kula wa kuma su rika tambayoyi lokacin da bukatar hakan ta taso. A rika sanar a hukumomin tsaro cikin gaggawa duk lokacin da ake zargin wani na aikata laifi saboda a dauki mataki," in ji Afunanya.

Momoh wanda ke da aure da yaya, ya amsa cewa ya yi laifin da ake zarginsa. Ya kuma ce ya yi aiki a fadar shugaban kasa daga 2013 zuwa 2014.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel